✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Annobar Kyanda ta kashe yara 14 a Anambra

Cutar ta bulla ne a Kananan Hukumomin Jihar tara

Gwamnatin Jihar Tutar Kyanda da ta bulla a Kananan Hukumomi tara da ke Jihar ta kashe yara 14.

Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dokta Afam Obidike, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, inda ya ce an samu rahoton kamuwar yara 414 daga Kananan Hukumomi tara da suka kamu da Kyandar.

Kwamishinan ya kuma ce inda lamarin ya fi ta’azzara akwai Anambra ta Gabas, da ta Yamma da Ayamelum da ihiala da Idemili ta Arewa da Nnewi ta Arewa, sai Onitsha ta Arewa da Njikoka, sai kuma Oyi.

Obidike ya ce tallafin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) sun taimaka wajen dakile yaduwar annobar.

Kwamishinan ya kuma ce yara 19,609 ne da ke wata 59 zuwa kasa da a baya ba a yi musu rigakafi ba aka yi musu a yanzu.

Kazalika ya ce unguwannin da ke kusa da inda annobar ta bulla ma an musu rigakafin domin dakike yaduwarta.