Antonio Guterres zai ziyararci Najeriya ranar Talata | Aminiya

Antonio Guterres zai ziyararci Najeriya ranar Talata

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres
    Sani Ibrahim Paki
Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres zai fara wata ziyarar aiki a wasu kasashen Afirka ta Yamma guda uku, cikinsu har da Najeriya.
Ana sa ran Mista Guterres zai fara ziyarar, wacce ya yi wa lakabi da ta azumi a ranar Asabar, kuma zai ziyarci Najeriya da Senegal da kuma Jamhuriyar Nijar.
Ana sa ran isowar shi Najeriya dai ranar Talata, inda zai tattauna da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Mataimakin Babban Magatakardar, Farhan Haq, shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a hedkwatar Majalisar da ke birnin New York na Amurka, inda ya ce ziyarar wani bangare ce ta ziyarar azumin bana da ya saba yi duk shekara.

Antonio Guterres dai ya fara ziyarar ce tun lokacin yana Babban Jami’in Kula da ’Yan Gudun Hijira, amma annobar COVID-19 ta kawo cikas ga ziyarar ta shi.

Farhan Haq ya ce yayin ziyarar tasa a Najeriya, Mista Guterres zai yi amfani da damar wajen jajanta wa wadanda ayyukan ta’addanci suka shafa a kasar da ma yankin baki daya, da ma yadda yakin Ukraine ke shafar nahiyar Afirka.

“Zai tattauna wadannan kalubalen tare da shugabannin da zai ziyarta.

“Ana sa ran zai fara sauka a kasar Senegal da yammacin Asabar. Daga nan kuma zai wuce Jamhuriyar Nijar ranar Litinin, sai kuma ranar Talata ya karasa Najeriya,” inji Farhan Haq.

Ya kuma ce Magatakardar zai yi buda-baki da Shugaba Macky Sall na Senegal, sannan zai yi bukukuwan karamar Sallah da Shugaban Nijar, Mohammed Bazoum.

Farhan ya kuma ce Antonio zai tattauna manyan jami’an gwamnati da kungiyoyin fararen hula da na mata da matasa da na shugabannin addinai.