Daily Trust Aminiya - Anya Tuchel ya karbi Chelsea a sa’a kuwa?
Subscribe

Anya Tuchel ya karbi Chelsea a sa’a kuwa?

Thomas Tuchel ya karbi ragamar horas da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a ranar Talata, bayan kungiyar ta sallami Frank Lampard saboda gazawa.

Sai dai sabon kocin na Chelsea ya fara buga wasa ba tare da yin nasara ba.

Chelsea ta kara da kungiyar Wolves a daren ranar Labara a gasar cin kofin Firimiya, inda aka tashi babu ci.

Duk da cewa wasan Tuchel na farko ke nan a matsayin kocin Chelsea, amma wasu na ganin ba ta sauya zani ba.

Yanzu haka Chelsea ta yi nasara a wasa daya daga cikin wasanni bakwai da ta buga a Firimiya.

Kungiyar ta sallami Lampard ranar Litinin, bayan ya shafe watanni 18 ba tare da cimma nasarar da kungiyar ke sa rai ba.

Tuchel, kafin zamansa kocin Chelsea, ya horas da kungiyar kwallon kafa ta Dortmund da ke kasar Jamus.

Daga bisani ya koma PGS a matsayin kocinta, kafin ita ma ta sallame shi a watan da ya gabata, sakamakon gazawa.

More Stories