✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

APC ce ta shirya shirme da sunan sakamakon zaben kananan hukumomin Katsina – PDP

Jam’iyyar PDP ta ce za ta garzaya kotu domin kalubalantar sakamakon zaben kananan hukumomin Jihar Katsina na ranar Litinin. Mukaddashin Shugaban jam’iyyar, reshen jihar, Salisu…

Jam’iyyar PDP ta ce za ta garzaya kotu domin kalubalantar sakamakon zaben kananan hukumomin Jihar Katsina na ranar Litinin.

Mukaddashin Shugaban jam’iyyar, reshen jihar, Salisu Uli, ya bayyana zaben da sakamakon da hukumar zaben jihar ta sanar a matsayin tsantsagwaron soki-burutsu, hasali ma ba a gudanar da zaben a kananan hukumomi akalla 11 ba a jihar.

Ya yi zargin cewa jam’iyyar APC mai mulki a jihar ce ta zauna ta tsara jerin sunayen da aka sanar a matsayin sakamakon zabe ba tare da wata shaida ko alkaluma ba.