✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC da PDP sun tsayar da ’yan takarar zaben cike gurbi na Jos da Bassa

Jam’iyyun APC da PDP sun gudanar da zaben ’yan takararsu a zaben cike gurbi na Dan Majalisar Wakilai mai wakilatar Mazabar Jos ta Arewa da…

Jam’iyyun APC da PDP sun gudanar da zaben ’yan takararsu a zaben cike gurbi na Dan Majalisar Wakilai mai wakilatar Mazabar Jos ta Arewa da Bassa da ke Jihar Filato, da za a gudanar a ranar 26, ga wata Fabrairu da muke ciki.

Shi dai wannan zaben cike gurbi za a gudanar da shi ne sakamakon rasuwar dan majalisar da ke wakiltar mazabar, marigayi Alhaji Haruna Maitala, wanda ya rasu a daren ranar Juma’a 2 ga watan Afrilun 2021, a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Abuja zuwa Jos.

Tsawon lokaci da aka dauka ba a gudanar da zaben ciken gurbin kujera ba, ya janyo wasu ’yan wannan mazaba, sun ta korafe-korafe, ganin cewa a doka bayan majalisa ta sanar da rasuwar dan majalisar, a cikin wata uku hukumar zabe take shirya zaben cike gurbi.

Tun da farko jam’iyyar APC ta shirya gudanar da zaben tsayar da dan takararta ne karkashin Shugaban Kwamitin Shirya Zabe, Horabul Abu Ajiya, aka kuma gudanar a Otal din Lamonde da ke garin Jos.

Amma sai ya kasance ’yan takara biyu da suka tsaya, tsohon Kwamishinan  Kasuwanci na Jihar Filato, Joseph Abbey da Honorabul Suleiman Yahaya Kwande suka yi kunnen doki, da kuri’a 344 kowannensu.

Saboda haka aka sake gudanar da zabe, a tsakaninsu a ranar Juma’a a garin Bassa.

Da yake bayyana sakamakon zaben a daren Asabar, bayan kammala zaben, shugaban kwamitin zaben, Honarabun Abu Ajiya ya bayyana cewa Joseph Abbey ya sami kuri’a 809, Honarabul Suleiman Yahaya Kwande kuma ya sami kuri’a 74. Saboda haka Honarabul Joseph Abbey ne ya lashe zaben

Ita ma a nata bangaren, jam’iyyar PDP ta zabi dan Majalisar Dokokin Jihar Filato mai wakiltar mazabar Irigwe da Bassa, Honarabul Musa Agah, a matsayin dan takararta a zaben cike gurbin.

Da yake bayyana sakamakon zaben da suka gudanar a Otel Lamonde da ke garin Jos, Shugaban Kwamitin Shirya Zaben, Honarabul Francis Orogu, ya bayyana cewa Honarabul Musa Agah ya sami kuri’a 152, a yayin da abokin takararsa, Honarabul Jonathan Dabo, ya sami 127. Don haka Honarabul Musa Agah ne ya lashe zaben.