✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘APC na nan daram ko bayan Buhari’

Alamar ita ce yadda ’yan siyasar Kudu maso Yamma ke dawowa APC

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, Ustaz Abubakar Yunus, ya ce APC jam’iyya ce mai adalci wacce ko Shugaba Buhari ya gama wa’adinsa, mafarkin da wasu ke yi na rushewarta ba zai zama gaskiya ba.

A zantawara da Aminiya, dan majalisar ya yi nuni da yadda wasu Gwamnonin Kudu maso Gabas da suka san siyasa ke barin jam’iyyarsu ta PDP suna dawowa APC.

Dan majalisar ya ce, “APC za ta rungumi kowa a tafi tare da shi, shi ya sa jam’iyyar ta rushe shugabanninta bayan cikar wa’adinsu, ta nada na riko don ta karfafa jam’iyyar, wanda hakan zai haifar mana da da mai ido.”

Ya kara da cewa tsarin karba-karba yana nan amma tsari ne da za a iya sauya shi ko a tabbatar da shi.

“’Yan Kudu da ke yunkurin dawowa APC sun hango ne cewa ita ce za ta sake dawowa a 2023.”

Ya ce, “batun idan Buhari ya gama APC za ta rushe, ai da ma farin jininsa ne, to tunda an yarda Allah ne Ya kawo shi, a lokacin da ake kyamar sa a 2023 ma Allah Zai iya kawo wanda ya fi shi,” inji shi.