✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta dage taronta na zaben dan takarar shugaban kasa

Yanzu taron zai gudana daga ranar Litinin 6, zuwa Laraba 8 ga watan Yuni, 2022.

Jam’iyyar APC mai mulki ta dage taron zaben dan takarar shugaban kasarta zuwa ranar Litinin 6 ga watan Yuni, 2002.

Sakataren Yada Labaran APC na Kasa, Barista Felix Morka ya ce, sabanin kwana biyu da jam’iyyar ta shirya gudanar da taron a baya, yanzu taron zai gudana ne a cikin kwana uku, dagar ranar Litinin 6, ga zuwa Laraba, 8 ga watan Yuni, 2022.

Sanarwar da ta fitar ta ce, “Sakamakon karin wa’adin da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi na mika sunayen ’yan takarar jam’iyyu, jam’iyyar APC na sanar da dage babban taronta na zaben dan takarar shugaban kasa da ta shirya ranar Lahadi 29 zuwa Litinin 30 ga Mayu, 2022, ya koma daga ranar Litinin 6 zuwa Laraba, 8 ga watan Yuni, 2002.”

Ya sanar da hakan ne a jajibirin ranar taron, wanda da farko jam’iyyar ta shirya gudanarwa ranar Lahadi, 29 zuwa Litinin 30 ga Mayu, 2022.

Hakan kuma na zuwa ne a ranar ta babban jam’iyyar adawa da PDP za ta fara gudanar da nata taron a Abuja.