✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

APC ta dage yakin neman zaben shugaban kasa a Kano

Mako biyu kafin zaben shugaban kasa, Jam'iyyar APC mai mulki ta dage yakin neman zaben shugaban kasa a Kano, har sai abin da hali ya…

Mako biyu kafin zaben shugaban kasa, Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta dage taronta na yakin neman zaben shugaban kasa a Jihar Kano, har sai abin da hali ya yi.

Da farko jam’iyyar ta shirya gudanar da gangamin yakin neman zaben ne a ranar Alhamis 16, ga watan Fabrairun da muke ciki, kimanin kwana 10 kafin zaben shugaban kasa ranar 25 ga wata.

Da yake tabbatar da dage taron, Daraktan Yada Labaran Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na APC, Festus Keyamo, ya shaida wa wakilinmu a ranar Juam’a cewa, “Gaskiya ne, har yazu ba a sanya rana ba,” domin gudanar da taron.

Mun nemi sanin dalili, amma Festus Keyamo ya ce, “Sauye-sauye aka samu abin da aka shirya.”

An dage taron ne kimanin mako biyu bayan ziyar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kai jihar, inda ya kaddamar da wasu manyan ayyuka a ranar 30 ga watan Janairu.

Sai dai ziyarar ta Buhari — wanda ya yi alkawarin jagorantar yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu — ba ta yi armashi ba.

Jama’a ba su yi dafifin tarbarsa yadda aka saba ba a Kano, jihar da APC ke bugun tunkaho da ita da kuma tunanin samun ruwan kuri’u kamar a zabukan da suka gabata; A zabukan shugaban kasa na 2015 da 2019 APC ta samu a Kano fiye da ko’ina a fadin Najeriya.

Mutane da dama sun bayyana rashin fitowar mutane tarbar Buhari a matsayin alamar raguwar farin jininsa a Kano, a yayin da wasu ke danganta lamarin da canjin kudi da gwamnati ta yi, wanda ya sa samun tsabar kudi gagarar yawancin ’yan Najeriya.

Sai dai a wani martaninta, Fadar Shugaban Kasa, ta ce har yanzu Shugaba na nan da farin jininsa a wurin Kanawa.

Jihar Kano dai na da muhimmanci a zaben shugaban kasa, inda jihar ke kan gaba a Arewa kuma ta biyu a Najeriya wajen yawan masu katin zabe, ga shi kuma dan asalin jihar kuma tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwako, ya fito takarar shugaban kasa a Jam’iyyar NNPP.