✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

APC ta dakatar da Aisha Binani a Adamawa

Kwamitin ya dakatar da ita kan rashin bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi.

Jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Yola ta Kudu ta dakatar da ‘yar takarar Gwamnan jam’iyyar, Sanata Aishatu Dahiru Ahmed Binani na tsawon watanni shida saboda rashin halartar kwamitin ladabtarwa kan wasu zarge-zargen da ake mata.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar a ranar Juma’a, mai dauke da sa hannun mambobin zartaswa 21 na jam’iyyar daga sassa daban-daban na Yola.

Sanarwar ta ce dakatarwar ta fara aiki daga ranar Juma’a 17 ga Fabrairu, 2023.

Kazalika, jam’iyyar a Karamar Hukumar ta samu korafi game da Sanata Aishatu Dahiru Ahmed Binani daga wani jigo a jam’iyyar a mazabar Bako, Auwal Hamma Adama Bawuro, bisa zarginta da haddasa rashin hadin kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.

Sanarwar ta ce dakatarwar ta biyo bayan wani kuduri ne da kwamitin Karamar Hukumar Yola ta Kudu, ya yi kan rashin gurfanarta a gabansa don kare kanta.

Da yake zantawa da manema labarai a Yola, shugaban jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Yola ta Kudu, Alhaji Ahmed Mohammed Mbamoi, wanda ya tabbatar da dakatarwar ya roki shugabannin jam’iyyar na jihohi da su yi la’akari da dakatarwar domin ta zama izina ga sauran ‘ya’yanta.