✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta dakatar da Orji Kalu ‘yan sa’o’i kafin zabe

An dakatar da shi ne saboda rashin biyayya da yi wa jam'iyya zagon kasa

Yayin da ya rage kasa da sa’o’i 24 kafin zabe, Jami’iyyar APC ta dakatar da Mai Tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu kan zargin yi wa jam’iyya zagon-kasa da sauran laifuffuka.

APC ta ce dakatarwar da ta yi wa Sanatan mai wakiltar Abiya ta Arewa ta nan take ce kamar yadda ta bayyana a cikin wasikar da ke dauke da bayanin ranar Juma’a.

Tun ba yau ba ake samun takun-saka tsakanin Kalu, wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Abiya ne da shugabannin APC a Jihar, inda ake zargin shi da yi wa jam’iyyar zagon-kasa a jihar.

Wasikar mai dauke da kwanan wata 21 ga watan Fabrairu, ta nuna an dakatar da Kalu daga jam’iyyar ne saboda “rashin biyayya da yi wa jam’iyya zagon kasa.”

A cewar APC, kafin daukar wannan mataki, “sai da aka gudanar da bincike mai zurfi da kuma shawarwari daga Kwamitin Ladabtarwar na gundumar Igbere ‘A’ cikin Karamar Hukumar  Bende a Jihar ta kafa.”

Matakin da jam’iyyar ta ce ya yi daidai da Sashe na 21B(i-v) na Kundin Tsarin Mulkinta, wanda Kalu din ya saba wa.

Ana zargin Kalu da take-taken kai dan takarar Gwamna na APC a jihar, Cif Ikechi Emenike, kasa a zabe mai zuwa.

Haka nan, ana zarginsa da yi wa Jam’iyyar APP aiki a jihar, jam’iyyar da a karkashinta kanensa, Mascot Uzor Kalu, ke takarar Gwamnan jihar.

A wata tattaunawa da aka yi da shi ranar Talata, Kalu ya tabbatar da cewa lallai yana goyon bayan takarar kanin nasa, inda ya ce zai iya shugabancin jihar.

Shugaban Kwamitin ladabtarwa na APC a Jihar, Paul Nwabuisi da sakataren Kwamitin, Cif Chidi Avajah da kuma Shugaban APC na jihar, Kingsley Ononogbu, su ne suka rattaba hannu kan wasikar dakatar da Kalu din.