✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta gaza a harkar tsaro – Tsohon Ministan Buhari

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Barista Solomon Dalung ya ce jam’iyyar APC ta gaza cika alkawuran da ta yi wa ’yan Najeriya a harkar tsaro

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Barista Solomon Dalung ya ce jam’iyyar APC mai mulki ta gaza cika alkawuran da ta yi wa ’yan Najeriya a kan harkar tsaro, musamman ’yan arewa.

Solomon, wanda minista ne a wa’adin farko na mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ya ce jam’iyyar ta gaza cika daya daga cikin muhimman alkawuran da ta yi yakin neman zabe a kan su.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da Sashen Hausa na BBC a ranar Asabar inda ya ce kimar jam’iyyar ta zube a idanun ‘yan Najeriya kuma babu wanda zai sake amincewa da ita matukar ba ta yi gyara ba.

Ya ce, “Wanne irin mulki ne wannan ace sai ka biya ’yan bindiga kafin su kyale ka ka je gona? Yaya makomar Arewa za ta kasance a nan gaba in aka ce sai kowa ya biya kafin ya yi aiki a gonarsa?

“Yanzu hatta tafiya babu damar yin ta a yankin cikin kwanciyar hankali. Dole sai ka yi azumi ka yi addu’a kafin ka yi tafiya saboda ka je lafiya, ka dawo lafiya.

“Wannan bai taba faruwa a baya ba a tarihin Najeriya.

“Mun tsaya tsayin daka wajen ganin wannan gwamnatin ta kafu amma ita kuma ta gaza biya mana namu bukatun.

“Mun fadawa gwamnatocin baya gaskiya, dole wannan ma mu fada mata, hakkinmu ne mu fada musu gaskiya,” inji tsohon ministan.

Ya kuma ce yanzu haka APC na cikin mawuyacin hali kuma tana kokarin durkushewa inda ya ce shi tsohon dan jam’iyyar ne wanda yake jiran a fara sabuwar rijista domin sabunta tasa.