✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

APC za ta fara tantance masu takarar gwamna da Majalisa

Ranar Asabar APC za ta rantsar da kwamitin tare da fara tantance masu neman takarar Majalisar Tarayya.

A ranar Asabar Jam’iyyar APC mai mulki, za ta fara aikin tantance masu neman takarar kujerar gwamna da Majalisar Dokoki ta kasa a karkashinta.

Jam’iyyar ta ce za a fara aikin tantacewar ne jim kadan bayan taron  kaddamar da shugabanni da sakatarorin kwamitin tantance masu neman takarar Majalisar Wakilai, Majalisar Dattijai da kuma kujerar gwamna.

Sakataren jam’iyyar na kasa, Sulaiman Argungu, ya sanar a safiyar Asabar cewa za a yi taron kaddamarwar ne da misalin karfe 12 na rana a otal din Fraser Suites da ke Abuja.

Argungu, ya ce daga bayan taron ne za a tantance masu neman takarar Majalisar Wakilai a ranar Asabar din, 14 ga watan Mayu, 2022, a otal din Zeus Paradise da ke Abuja daga karfe 2 na rana.

A ranar Lahadi 15 ga Mayu, 2022 kuma, za a gudanar da tantance masu neman takarar kujerar Sanata da masu neman kujerar gwamna a otal Fraser Suites, daga karfe 10 na safe.