✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC Ta Karbi Daruruwan Magoya Bayan PDP a Katsina

Daruruwan magoya bayan Jam’iyyar PDP ne suka sauya sheka zuwa APC a Katsina. Daraktan Yada Labaran Kwamitin Yakin Neman Zaben APC na jihar, Ahmad Abdulkadir…

Daruruwan magoya bayan Jam’iyyar PDP ne suka sauya sheka zuwa APC a Katsina.

Daraktan Yada Labaran Kwamitin Yakin Neman Zaben APC na jihar, Ahmad Abdulkadir ne ya bayyana hakan a Katsina.

Abdulkadir ya ce shugaban jam’iyyar ne ya karbi magoya bayan yayin taron yakin neman zaben dan takara Gwamnan Katsina na APC Dikko Radda a Mashi.

“Ya zuwa yanzu dan takarar ya ziyarci kananan hukumomi shida daga cikin 12 da ke mazabar Katsina ta Arewa. Ya kuma ziyarci unguwanni sama da 60 a yankunan shida.

“A Daura kuma, ya ziyarci Shugaban Kasa inda ya shaida masa dalilin kai ziyarar, da nufin gane wa idonsa halin da mutane ke ciki da nufin samun bayanai a kai a kai kan inda za a bukaci kulawar sa idan ya zama Gwamna”, in ji shi.

Ya kuma ce Buhari ya yaba da kokarinsa tare da nuna kwarin gwiwar cewa zai lashe zaben Gwamnan jihar.