✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta shawarci PDP ta rufe ofishin uwar jam’iyyarta

Jam'iyyar APC mai mulki ta shawarci PDP akan ta kulle ofishin uwar jam'iyyar matukar ba zata iya biyan ma'aikatam jam'iyyar ba.

Jam’iyyar APC mai mulki ta nemi jam’iyyar adawa ta PDP da ta rufe hedikwatarta matukar ba za ta iya biyan ma’aikatanta hakkinsu ba.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da Mataimakin Sakataren Yada Labaran APC, Yekini Nabena ya fitar.

“Kwanan nan sakatariyar jam’iyyar ta kori wani mutum da ke aiki da ita.

“Rashin adalci jam’iyyar ya sa ta kori kaso 50 na ma’aikatanta”, inji shi.

Jam’iyyar APC ta ce jam’iyyar da ba ta biyan ma’aikata albashi amma tana ba su damar yin tawaye a cikin azaba, bai kamata a zabe ta a kan mulki ba.

Wasu daga cikin ma’aikatan da aka sallama tuni sun maka PDP a Kotun Sasanta Rikicin Ma’aikata ta Kasa, domin neman hakkinsu.

APC ta kara da cewa yana daga cikin zalunci ka ki biyan ma’aikaci hakkinsa bayan ya maka aiki.

Ta kara da cewa babu abinda PDP ta iya face farfaganda.

Rahotanni sun bayyana cewa tun bayan rasa mulki da jam’iyyar ta yi, ta kasa biyan ma’aikatanta wasu alawus-alawus dinsu.

Da yake mayar da martani a wata hira ta wayar tarho da wakilinmu, Sakataren Yada Labaran PDP na Kasa, Kola Ologbondiyan ya ce, “ba abin da (APC) ta ke yi face hauragiya”.