✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta soke takarar mutum 10 cikin masu neman kujerar Shugaban Kasa

APC ta ce mutum 10 daga cikin 23 da ke neman tikitin takarar ba su cancanta ba.

Jami’yyar APC mai mulki a Najeriya ta soke takarar mutum 10 daga cikin 23 da ke neman tikitin takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar a zaben 2023 da ke tafe.

Kwamitin tantance manema takarar kujerar Shugaban Kasa karkashin jagorancin tsohon shugban jam’iyyar na kasa, Cif John Odigie-Oyegun ne ya sanar da hakan a yammacin ranar Juma’a.

Bayanan soke takarar mutanen, na zuwa ne yayin da jagoran kwamitin, Cif John Odigie-Oyegun ya mika rahotonsa ga shugaban jam’iyyar na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, yana mai shaida masa cewa mutum goman da aka soke takararsu ba su cancanta ba.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa, Cif Oyegun ya ki ba da sunayen wadanda aka soke takararsu a lokacin da manema labarai suka tambaye shi.

Kadan daga cikin wadanda suke neman takarar shugabancin Najeriya karkashin jam’iyyar wacce ta kwashe shekara bakwai tana mulki, akwai Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, tsohon Gwamnan Jihar Legas, Ahmed Bola Tinubu da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan.

Akwai kuma Gwamnonin APC biyar da suka shuga sahun manema takarar Shugaban Kasa da suka hada da: Kayode Fayemi (Ekiti) da Yahaya Bello (Kogi) da Abubakar Badaru (Jigawa) da Dave Umahi (Ebonyi) sai kuma Ben Ayade (Kuros Riba).

Aminiya ta ruwaito cewa, ‘yan takara 23 ne kwamitin tantancewar karkashin jagorancin Cif John Odigie-Oyegun ya tantance a katafaren otel din nan na Transcorp Hilton da ke Abuja a ranakun Litinin da Talatar da suka gabata.

Sai dai gabanin yanzu, tun bayan kammala aikin tantancewar awanni 72 da suka gabata, ‘yan takarar da ma magoya bayansu sun shiga dar-dar saboda rashin bayyanar da sakamakon.