Daily Trust Aminiya - APC ta taimaka mana da ta tsaida Yahaya Bello dan takara – P
Subscribe

APC ta taimaka mana da ta tsaida Yahaya Bello dan takara – PDP

Jam’iyyar PDP ta ce babban abin da ke yi mata dadi game da zaben Jihar Kogi da za a yi kwanan nan shi ne yadda Jam’iyyar APC mai mulki, ta tsayar da Gwamna Yahaya Bello dan takararta a zaben.

Kakakin Jam’iyyar PDP a Jihar Kogi, Mista Bode Ogunmola, ya bayyana haka inda ya ce Allah ne Ya amshi addu’arsu, har APC ta tsayar da Yahaya Bello, domin kuwa za su yi fata-fata da shi a zaben Gwamnan da ke tafe.

Ya ce “Bama tunanin akwai koda karamar hukuma daya da Yahaya Bello zai yi nasara a zaben Gwamnan Jihar da za gudanar a watan Nuwamba. Mutanen jihar sun dandana kudarsu bayan darewarsa kujerar Gwamnan Jihar. Ba sai an yi wa wani tuni ba. A dalilin haka nake so kowa ya sani cewa ba mu da fargaba ko kadan a zaben Gwamnan Jihar da ke tafe, Idan ya iya bi ta kan shugabannin jam’iyyarsa da wakilai masu zaben dan takara har suka iya tsaida shi, ba zai samu haka ba a wajen mutanen Jihar Kogi domin kowa ya shaida irin bakar wahalar da aka shiga a tsawon mulkinsa.”

Da yake mayar da martani a kan wanna matsayi na Jam’iyyar PDP, Daraktan Watsa Labarai na Gwamna Yahaya Bello, Mista Kingsley Fanwo, ya bayyana cewa a shirye suke domin tunkarar zaben da ke tafe, kuma su ne suke da nasara.

More Stories