✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta yi mana fashi a zaben kananan hukumomin Adamawa – PDP

’Ya’yan Jam’iyyar PDP a karamar Hukumar Gombi da ke Jihar Adamawa sun zargi Jam’iyyar APC da kasancewa jam’yya ta ’yan fashi.’Ya’yan Jam’iyyar ta PDP sun…

’Ya’yan Jam’iyyar PDP a karamar Hukumar Gombi da ke Jihar Adamawa sun zargi Jam’iyyar APC da kasancewa jam’yya ta ’yan fashi.
’Ya’yan Jam’iyyar ta PDP sun fadi hakan ne ga manema labarai, bayan bayyana sakamakon zaben kananan hukumomin jihar da aka yi inda Jam’iyyar APC ta yi nasarar lashe zaben kananan hukumomi 18 daga cikin 21 da ke jihar da gagarumar nasara. Shugaban Jam’iyyar PDP na karamar Hukumar Gombi, Malam Ahmad A. Abbo ya ce “Jam’iyyar APC tana nuni da cewa tana yaki da cin hanci da rashawa amma ban taba ganin mafi munin cin hanci da rashawa kamar na zaben kananan hukumomin da aka yi a Jihar Adamawa ba musamman a karamar Hukumar Gombi.”
Magoya bayan Jam’iyyar PDP sun yi zargin cewa wani tsohon Sakataren karamar Hukumar Gombi ya cika motarsa da kayayyakin zabe kuma sun ce suna ganin doka aka ba shi daga sama domin aikata wadannan abubuwa.
Sun kara da cewa akwai wani James wanda shi kadai ya rika dangwala hannu a kan kuri’u na unguwanni uku sannan ya dauki akwatin zaben zuwa Gombi da ya taso daga Guyuk. “Wadannan labaran sun iso mu daga unguwanni goma inda aka ce an riga an dangwala kuri’u a cika a akwatuna zabe na unguwanni goma,” inji shi.
Ya kara da cewa “A cikin wuraren jefa kuri’a 114 na karamar hukumar bakwai ne kawai aka gani suna aiki lokacin jefa kuri’un. Shin unguwanni uku za su iya zaben kansila ne ko kuma unguwanni bakwai a cikin 144 da aka kayyade za su iya zaben shugaban karamar hukuma ne?”
Ya ce a cikin unguwanni 10 babu inda aka yi zabe kuma babu sakamako sannan babu wani wurin da aka ga ana jefa kuri’a.
Ya ce wannan abin kunya da Jam’iyyar APC ta yi shi ne ya sa za su fadi kai-tsaye cewa kirarin da take yi na cewa “Adalci” a Jihar Adamawa karya ne domin suna fadi babu cikawa.
Ya ce Mukaddashin Shugaban Hukumar Zaben bai cancanci wannan mukami ba kuma ya nuna gazawa don haka bai kamata a rika nada mutane irinsa a irin wadannan kujeru masu muhimmanci ba. “Don haka muna rokon a ciree shi daga kan kujerar ta mukaddashin shugaban hukumar zaben ta jihar da sauran shugabannin hukumar na kananan hukumomi domin ba su yi adalci a zaben ba,” inji shi.
Sai dai wani jigo a Jam’iyyar APC da ya fito daga karamar Hukumar Gombe, Alhaji Ahmed Rufa’i ya ce Jam’iyyar PDP ta riga ta mutu ba a Jihar Adamawa kadai ba a kasar baki daya. “Su dai sun kasance marasa sa’a ne kawai domin kafin wannan zaben ai an yi wasu zabubbuka kuma ba su ci ba. Tun daga zaben Shugaban kasa har zuwa na kananan hukumomi babu mutum daya da yake daga Jam’iyyar PDP a Gombi da ya taba cin zabe,” inji shi