✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC za ta bude yakin neman zaben Shugaban Kasa da addu’o’i na musamman

A ranar Laraba ce dai jam'iyyar za ta fara yakin neman zaben

Jam’iyyar APC mai mulki za ta kaddamar da yakin neman zabenta na Shugaban Kasa da addu’o’i na musamman da kuma tattakin zaman lafiya a Abuja ranar Laraba.

Daraktan Yada Labaran Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa (PCC), Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanrwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin.

A cewar sanarwar, “A madadin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, muna godiya ga dukkan ‘yan kwamitin yakin neman zaben Shugaban Kasarmu, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, da Mataimakinsa, Kashim Shettima, bisa gudummawarsu ta jiki da aljihu ba tare da gajiyawa ba, domin nasarar jam’iyar a zaben 2023.

“Kuma muna sanar da mambobinmu cewa za a gudanar da tattakin zaman lafiyar ne da zarar an kammala addu’o’in na musamman.

“Nadin da aka yi a kwamitin kuma, don yi wa jam’iyya hidima ne, kuma muna bukatar cikakkiyar sadaukarwa daga kowa.

Haka kuma kwamitin zai yi aiki da dukkain kungiyoyin jam’iyyar, domin yakin neman zabe.

“Muna kuma karfafa guiwar sauran kungiyoyin da har yanzu ba su yi rajista tare da PCC din ba, da su yi hakan da gaggawa nan don tafiya tare,” inji Daraktan.