✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC za ta kwace gwamnati daga hannun PDP a Sakkwato —Shugaban Matasa

Muna ci gaba da fadi-tashin ganin Jihar Sakkato ta sake komawa karkashin jagorancin jam’iyyar APC.

Shugaban Matasan APC na Arewa maso Yamma, Abdulhamid Muhammad ya sha alwashin cewa jam’iyyar za ta karbe madafar iko daga hannun jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Sakkwato.

A wata sanarwa da ya fitar yayin ganawa da manema labarai, ya ce yankin Arewa maso Yamma zai kasance mallakin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Zaben 2023 da ke tafe.

Mohammad ya ce suna ci gaba da fadi-tashin ganin Jihar Sakkato ta sake komawa karkashin jagorancin jam’iyyar APC.

Ya bayyana cewa, jam’iyyar za ta ci gaba da rike madafan iko a sauran jihohin da APC ke mulki a shiyyar Arewa maso Yamma.

A cewarsa, “tuni da dama daga cikin makusantan Gwamna Aminu Tambuwal suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

“Muna sa ran da Yardar Allah da yawa daga cikinsu za su ci gaba da ficewa daga jam’iyyar adawa kafin Babban Zabe.

“Wannan ya nuna cewa APC ta ci gaba da zama jam’iyyar da za ta iya lashe zabe a duk yankin Arewa maso Yamma da ma Najeriya baki daya.

Muhammad ya kuma ba da tabbacin cewa, APC tare da kokarin matasan yankin Arewa maso Yamma, za su jajirce wajen ganin duk mukaman da jam’iyyun adawa ke rike da su a Jihar Sakkwato da sauran Majalisun Dokokin jihar sun dawo hannun APC.

“Ba wai kawai za mu sasanta ba ne, za mu tabbatar da cewa duk ‘yan Majalisar Wakilai na PDP da ke wakiltar jihohin Arewa maso Yamma a Majalisun Tarayya ba su dawo ba.

“Za mu mayar da su [’yan PDP] gidajensu, wadannan ’yan jam’iyyar adawa da suka mamaye kujerun zaurenmu na alfarma daga Arewa maso Yamma ba sa mana wakilci mai inganci,” inji Mohammad.

“Muna da yakinin cewa bayan tabbatar wa APC yankin Arewa maso Yamma baki daya, jami’yyar za ta yi nasara a sauran jihohin da ke shiyyoyin siyasar kasar nan a zaben na 2023.

“Za mu kwato jihohin Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu da Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya wadanda ke karkashin jam’iyyun adawa.”