✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aramco: Hannun jarin kamfanin man Saudiyya ya yi tashin gwauron zabo

Darajar hannayen jarin Aramco ta karu zuwa Riyar 42.9.

Farashin hannayen jarin kamfanin mai na kasar Saudiyya, wato Aramco, ya yi tashin gwauron zabo zuwa Dala 11 a sakamakon rikicin Rasha da Ukraine da ya haddasa tashin farashin man a kasuwannin duniya.

Kasuwar hadahadar hannayen jarin Saudiyya, Saudi Tadawul, ta sanar a ranar Laraba cewa darajar hannayen jarin Aramco ta karu zuwa Riyar 42.9.

Kafin nan Riyal 32 (ko Dala 8.53) ne farashin kowane hannun jarin Aramco, kamfanin da gwamnatin Saudiyya — kasar da ta fi arzikin danyen mai a duniya — take da mafi rinjanyen hannayen jari.

A ranar Laraba farashin gangar danyen mai samfurin Brent ya tashi zuwa Dala 113, sa’o’i kadan bayan an wayi gari yana Dala 110.18; danyen mai samfurin WTI da aka wayi gari yana Dala 110.18 kuma ya tashi zuwa Dala 110.50. 

Kamfanoni da gwamnatoci na kara shiga damuwa saboda tunanin rikicin na Rasha da Ukraine na iya haddasa karancin mai.

Rasha dai ita ce kasa ta biyu mafi yawan arzikin danyen mai a duniya, sanna ita ce ta daya a bangaren iskar gas a nahiyar Turai.

Duk da cewa Saudiyya ce ja-gaba a arzikin mai a duniya, amma Rasha ce ta fi taka rawar gani da kuma-fada-a-ji a bangaren, a ciki kasashe 10 mafiya arzikin mai da manyan kamfanonin (OPEC+).

Masu ruwa da tsaki a bangaren makamashi na dakon sakamakon taron OPEC+ inda ake tattaunawa kan yiwuwar kara adadin man da ake hakowa domin rage tsadar da ya yi a kasuwar duniya.