Arsenal na dab da kammala cinikin Raphinha daga Leeds | Aminiya

Arsenal na dab da kammala cinikin Raphinha daga Leeds

    Abubakar Maccido Maradun

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke kasar Ingila tana dab da kammala sayen dan wasan gaba dan kasar Brazil, Raphinha, daga kungiyar Leeds United.

Hakan dai ya faru ne kasancewar Barcelona ta ja baya a zawarcin dan wasan mai shekara 25 da haihuwa, kamar yadda kafar Goal.com ta ruwaito.

Kazalika, ana ganin hakan ba ya rasa nasaba da matsin tattalin arziki da kungiyar ta Barcelona ke fama da shi a halin yanzu.

Ana dai cinikin dan wasan ne a kan Yuro miliyan 58.