Daily Trust Aminiya - Arsenal ta dauki Albert Sambi daga Anderlecht

Albert Sambi Lokonga

Arsenal ta dauki Albert Sambi daga Anderlecht

Arsenal ta kammala daukar dan kwallon Belgium, Albert Sambi Lokonga daga Anderlecht kan yarjejeniya mai tsaho.

Sai dai ba a fayyace kudin da aka sayi dan kwallon ba, amma ana hasashen cewar ya kai dalar Amurka miliyan 17.2.

Tun yana shekara 15 ya koma Anderlecht, kuma ya fara taka leda a kungiyar cikin watan Disambar 2017.

Ya zura kwallaye uku cikin wasanni 78 da ya haska a kungiyar.

Mai taka leda daga tsakiya wanda zai saka riga mai lamba 23 dauke da sunan Sambi, ya buga wa tawagar Belgium wasa ta matasa ‘yan kasa da shekara 21 inda ya ci kwallo biyu.

Haka kuma, Arsenal ta kammala daukar dan wasan baya na kungiyar Brighton, Ben White kan fam miliyan 50 da kuma Nuno Tavares daga Benfica kan fam miliyan takwas.

Karin Labarai