✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arsenal za ta maye gurbin Arteta da Conte

Yanzu haka wasanni biyar kacal suka ragewa Arteta don ceton aikinsa.

Kungiyar Kwallon Kafa ta Arsenal ta soma nazarin kulla yarjejeniya da tsohon kocin Inter Milan da Chelsea, Antonio Conte domin maye gurbin kocinta na yanzu, Mikel Arteta.

Ya zuwa yanzu dai Arteta ya yi rashin nasara a wasanni 20 cikin 60 da ya jagoranta, lamarin da ya sanya matsin lambar neman korarsa ke karuwa a Arsenal.

Matsin lambar na karuwa musamman biyo bayan rasa wasanni biyu jere da juna a farkon kakar wasa ta bana, da suka hada da rashin nasara a wasan ta da Brentford da 2-0, sai kuma Chelsea da ta lallasa ta har gida da wasu kwallayen 2-0.

Cikin watanni 20 da ya shafe yana jagorantar kungiyar, Arteta ya jagoranci Arsenal zuwa kare Firimiyar Ingila a matsayi na takwas cikin kakanni biyu a jere da juna, lamarin da ya sanya Gunners ta rasa samun gurbin buga wasannin Turai karon farko cikin shekaru 25.

A baya bayan nan Jaridar UK Telegraph ta ruwaito cewa, yanzu haka wasanni biyar kacal suka ragewa Arteta don ceton aikinsa na horas da Arsenal, kuma Antonio Conte tsohon kocin Inter Milan da Chelsea ke kan gaba cikin wadanda za su iya karbar jagorancin kungiyar ta Gunners.

Jaridar ta ce Arsenal ta bai wa Arteta daga yanzu zuwa karshen watan Oktoba ya sauya akalar bajintan kungiyar domin ceton aikinsa ko kuma ta nemo wanda zai maye gurbinsa.

A watannin baya ne dai aka rika alakanta Conte dan kasar Italiya da komawa gasar Firimiya don horas da kungiyar Tottenham Hotspur, amma yarjejeniyar ta gaza kulluwa.

Alkaluma sun nuna cewa Conte ya samu nasarar lashe wasanni 51 daga cikin 76 da ya jagoranci Chelsea a gasar Firimiya, inda kuma ya lashe kofin kakar shekarar 2016 da 2017.