✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arzikin attajirai 10 mafi kudi a duniya ya ninku bayan bullar annobar Coronavirus

Manyan attajirai 10 da suka fi kudi a duniya, ciki har da Jeff Bezos da Elon Musk da Bill Gates sun samu kudin da suka…

Manyan attajirai 10 da suka fi kudi a duniya, ciki har da Jeff Bezos da Elon Musk da Bill Gates sun samu kudin da suka kai Dala biliyan 500 bayan bullar cutar Coronavirus a duniya, inji wani sabon rahoton da cibiyar Oxfam ta fitar.

Rahoton ya gano cewa bullar cutar za ta kara haifar da wagegen ginin da ake da shi a tsakanin attajirai da talakawa a duniya idan gwamnatoci ba su dauki kwararan matakan bunkasa tattalin arzikin kasashensu ba.

Cibiyar Oxfam ta ce mutum dubu mafiya arziki a duniya sun maye gurbin hasarar da suka tafka a farkon bayyanar cutar sakamakon yadda kasuwannin hannun jari suka farfado.

A wani abu da ke akasin haka, Oxfam ta ce za a iya daukar fiye da kamar shekara 10 kafin matalauta a duniya su iya mayar da komadar tattalin arzkin da suka yi hasara a dalilin annobar.

Kungiyar ta ce manyan attajirai dubu a duniya sun yi hasarar kashi 30 na dukiyarsu sakamakon cutar, amma cikin wata 10 kacal sun mayar da hasarar.

Daga cikin wadanda suka fi samun bunkasar arziki akwai Jeff Bezos, wanda dukiyarsa ta karu da Dala biliyan 78; sai Elon Musk da Dala biliyan 129; sai Mark Zuckerberg da dukiyarsa ta ninka da Dala biliyan 45; sai kuma Bill Gates da dukiyarsa ta karu da Dala biliyan 22.

Oxfam ta yi ikirarin cewa manyan attajiran 10 za su iya samar wa kowane dan Adam a duniyar nan allurar rigakafin Coronavirus sau biyu, a farashin Dala biliyan 141.2 – wato kowace allura a kan Dala 9.

Sannan za su iya amfani da Dala biliyan 80 cikin dukiyarsu wajen ceto miliyoyin mutane a duniya daga kangin matsanancin talauci na shekara guda.

“Kasashe da mutane matalauta na azurta manyan attajiran duniya – wadanda ke amfana kuma suke jin dadin cutar, yayin da ainihin wadanda ke tunkarar cutar kamar kananan ma’aikata a manyan kantuna da jami’an kiwon lafiya da masu kasa kaya a kasuwanni – suke barje gumi domin biyan bukatun yau da kullum,” inji Gabriela Bucher, Babbar Daraktar Cibiyar Oxfam.