✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asarar N902.1m aka yi a gobarar Kasuwar Katsina —Kwamiti

’Yan kasuwa 685 sun yi asarar dukiyoyin da kimarsu ta kai miliyan N902.1 a gobarar.

Kwamitin bincike kan gobarar Babbar Kasuwar Katsina ya ce akalla ’yan kasuwa 685 ne suka yi asarar dukiyoyin da kimarsu ta kai miliyan N902.1 a gobarar.  

Shugaban Kwamitin binciko musabbabin gobarar ta ranar 22 ga watan Maris, Alhaji Tasiu Dandagoro ne ya bayyana haka yayin mika wa Gwamna Aminu Masari rahoton kwamitin ranar Laraba.

“Kwamitin ya gano kusan mutum 685 da lamarin ya shafa kai-tsaye, kuma wutar ta kone shaguna 605, banda na ’yan Kasuwa 59 da suke a rabe jikin wasu shagunan, sai kuma 21 da aka sace dukiyoyinsu yayin gobarar.

“Kimar dukiyar da aka yi asararta ta kai Naira miliyan N902.1 banda kudin ginin shagunan,” inji shi.

Dandagoro ya ce rashin kyakkyawan tsarin rarraba wutar lantarki zuwa shaguna shi ne ya haifar da tashin gobarar.

Shugaban kwamatin ya ci gaba da cewa bincikensu ya gano kasuwar ba ta da kayan kashe gobara na kota-kwana masu aiki, kuma babu rijiyoyin burtsatsai da za su taimaka wajen kashe wuta.

A kan batun sake gina shagunan kasuwar, Kwamitin ya ba gwamnati shawara kan ta gina shaguna dai-dai marasa bene guda 460 ko ta yi manyan gine-gine biyu da za su samar da shaguna 700.

Ya kuma shawarci gwamnatin da ta yi amfani da taswirar kasuwar na asali wanda bai yi tanadin shagunan wucin-gadi ba a kasuwar.

Da yake nasa jawabin, Gwamna Masari, ya gode wa Kwamatin kan hidimta wa Jihar da gudunmawarsa na ganin an sake farfado da kasuwar.

Masari, ya yi kira da mutanen Jihar da su nemi gafarar ubangiji saboda Jihar da kasa baki daya na fuskantar matsaloli da dama.