✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Asirin budurwar da saurayi ya yi garkuwa da ita ya tonu

Dubun wata budurwa mai shekaru 17 ya cika bayan ta hada baki da saurayinta, ya yi garkuwa da ita a kokarinsu na karbar kudi daga…

Dubun wata budurwa mai shekaru 17 ya cika bayan ta hada baki da saurayinta, ya yi garkuwa da ita a kokarinsu na karbar kudi daga hannun mahaifiyarta.

Ana zargin Seun Adekunle ‘yar unguwar Agura a Birnin Abeokuta da hada baki da saurayinta Basit Olasunkanmi ya yi garkuwa da ita, ya kuma nemi kudin fansa Naira dubu dari biyar daga mahaifiyarta.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ogun ta shaida wa Aminiya cewa mahaifiyar Seun mai suna Bukky Adekunle ce ta shigar da kara a caji ofis a ranar 4 ga watan Yuni, cewa ta aiki diyarta kasuwar Lafenwa tun ranar 1 ga watan amma ba ta kara ganin ta ba.

Kakakin Rundunar DSP Abimbola Oyeyemi ya ce wani mutum ya kira Bukky ta waya cewa ya yi garkuwa da diyarta, kuma yana neman ta biya Naira dubu dari biyar muddin tana so diyaryarta ta dawo gida.

“Hakan ta sa DPO Enugada Baba Hamzat, ya jagoranci jami’an ‘yan sandan da suka dukufa bunciken da ya kai ga kamo yarinyar da saurayinta a maboyarsu.

“Bincike ya nuna cewa saurayin mahauci ne, kuma shi ya rudi yarinyar domin karbar kudi a wajen mahaifiyarta domin baiya wa kansu wata bukata” inji shi.

Abimbola Oyeyeme ya kara da cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Ogun Kenneth Embrimson ya ba da umarnin tura saurayin da budurwarsa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar domin kammala bincike da grufanar da su a kotu.