✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ASUU: Gwamnatin Kano ta bukaci malaman jami’o’inta sun janye yajin aiki

Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci Kungiyar Malaman Jami'a (ASUU) reshen jami'o'inta da su koma bakin aiki.

Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) reshen jami’o’inta da su koma bakin aiki.

Gwamantin ta mika wannan bukatar ce a wata ganawa da ta yi da shugabannin ASUU na jami’ointa biyu a ranar Talata.

Taron wanda aka shafe awowi ana yi tsakanin bangarorin biyu, an tashi ba a cimma wata matsaya ba; Amma za a sake zama a mako mai zuwa — sai dai babu tabbacin haka.

Wakilinmu ya gano a  yayin zaman, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, Usman Bala Mohammed ya roki malaman jami’oin jihar da su koma bakin aiki, ko da za su dakatar da zama ’ya’yan kungiyar ne na watan uku.

Sai dai bangaren kungiyar ya ce hakan ba zai yiwu ba, domin ba za su iya tunkarar uwar kungiyar da wannan bukata ba.

A hirarsa da ’yan jaridu bayan taron, shugaban ma’aikatan jihar ya ce, babu wani mataki da za su dauka kan malaman jami’an a yanzu, amma idan tura ta kai bango za su san abin da za su yi.

A nasa bangaren Shugaban ASUU Reshen Jihar Kano, Abdulqadir Muhammad, ya ce, “Mun fada wa gwmnati gaskiya kan batun janyewa da kuma sake haduwarmu a mako mai zuwa; Sai dai daga uwar kungiya idan wani abu ya taso”.

 A jami’oin gwamnatin jihar guda biyu — Jami’ar Yusuf Maitama Sule da kuma ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil — ana ci gaba da ayyukan gudanarwa, amma banda koyarwa, kuma duk da haka gwamnatin jihar na ci gaba da biyan malaman albashinsu.