✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ASUU: Jami’ar Filato ta dakatar da albashin masu yajin aiki

Jami'ar Jihar Filato, ta ce ba za ta kara biyan malaman jami'ar da suke yajin aiki albashinsu ba

Hukumar gudanarwar Jami’ar Jihar Filato, ta bayyana cewa ba za ta kara biyan malaman jami’ar da suke yajin aiki albashinsu ba, har sai sun koma bakin aiki.

Magatakardar jami’ar, Mista Yakubu Ayuba ya ce wannan matsaya da aka dauka, tazo ne bayan umarnin da majalisar gudanarwar jami’ar ta bayar, a taron da ta gudanar a garin Jos.

Ya yi biyanin cewa, abubuwan da suka janyo har Kungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya (ASUU) da Kungiyar Ma’aikatan Jami’a ta Najeriya (SSANU) suka tafi yajin aikin, tuni an warware su.

“Gwamnati ta sanya hanu kan takardar yarjejeniya da ASUU kan abubuwa guda takwas, da suka kawo wannan yajin aiki tun a ranar 9 ga watan Augustan da ya gabata.

“Don haka ci gaba da yajin aikin ga malaman jami’ar ta Filato, suna yi ne don nuna biyayya ga uwar kungiyar ta kasa, ba don abin da ya shafe su ba.”

Ya ce don haka, Gwamnatin Jihar Filato da hukumar gudanarwar jami’ar, sun ba da umarnin kada a biya dukkan ’yan ASUU da NASUU da basu dawo bakin aiki albashinsu ba.

Ya ce za a raba rajistar rubuta sunayen wadanda suka dawo, a dukkan sassan jami’ar don ganin an yi aiki da umarnin da aka bayar.

Da yake magana kan wannan umarni, Shugaban ASUU reshen Jami’ar Jihar Filato, Dokta Monday Hassan, ya bayyana cewa za su ci gaba da yin biyayya ga uwar kungiyarsu, kan yajin aiki da suke yi.

Ya ce jami’ar ta amfana da ayyuka da dama, ta hanyar ASUU.

“Mu muna goyon bayan uwar kungiyarmu kuma za mu ci gaba da goyon bayanta, babu gudu babu ja da baya; Domin wannan jami’a ta amfana da ayyuka da dama ta hanyar wannan kungiya.”