✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ASUU na da hannu a rashawar da ake samu a bangaren ilimi —Buhari

Buhari ya bayyana damuwa kan abinda ya kira cin hancin da ya mamaye kudaden shigar da jami’oi ke tarawa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya zargi Kungiyar Malaman Jami’oi ta ASUU da hannu wajen cin hanci da rashawar da ake samu a bangaren ilimi.

Shugaban ya yi wannan zargi a jawabin da ya gabatar yayin taron da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC  da Hukumar Zana Jarabawar Shiga Jami’a ta JAMB suka shirya a ranar Talata.

A yayin taron, Buhari ya tattauna kan matsalolin da ke hana ruwa gudu a bangaren ilimin Najeriya, wadanda suka hana samar da yanayi mai kyau da matasa za su ci gajiyarsa.

A cewarsa, ta’asar rashawa da kungiyar ASUU ke tafkawa na kawo cikas ga kokarin da gwamnatin kasar ke yi wajen bunkasa bangaren da kuma tabbatar da ci gaba.

Buhari ya ce cin hancin da ya dabaibaye wannan bangaren, ya kauda idanun masu sukar gwamnatinsa dangane da irin kudaden da take zubawa domin inganta ilimi, inda suka mayar da hankali kawai akan kasafin kudin da ake ware wa bangaren.

Buhari ya ce yajin aikin da ake samu a bangaren manyan makarantun kasar kan nuna cewar gwamnati bata kula, ko ba da kudaden da ake bukata wajen bunkasa ilimi, alhali kuma ba haka abin yake ba, domin yajin aikin da ake samu na yi wa kokarin gwamnati zagon kasa.

Shugaban ya ce ya kamata a daina sanya ido kawai akan Kasafin Kudin da ake warewa bangaren ilimi, domin kuwa akwai wasu kafofi da gwamnati ke ba da makudan kudade domin samar da ilimi.

Ya zayyana kafofin ilimin da suka hada da bangaren ilimin firamare da ake kira ‘Basic Education’ da kudaden da Hukumar TETFUND ke karba tana gudanar da manyan ayyuka a Jami’oin kasar da kuma asusun harajin TETFUND da ke biyan makarantu kudaden da suke kashewa wajen gudanar da manyan ayyuka.

Buhari ya kuma bayyana damuwa a kan abinda ya kira cin hancin da ya mamaye kudaden shigar da jami’oi ke tarawa wanda masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi basa mayar da hankali akai.

Shugaban ya ce karancin kudaden da gwamnati ke samu ba zai bata damar ci gaba da daukar nauyin wadata bangaren ilimi da kudade ita kadai ba.

Ya yi kira ga manyan makarantun da suka hada da jami’oi da makarantun fasaha da kwalejojin ilimi da su zage dantse wajen janyo hankalin masu zuba jari da kuma ba da gudunmawa domin samun kudaden talllafin gudanar da bincike da kuma gudanar da wasu ayyuka a cikin manyan makarantun.