✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nan da awa 48 za mu sake tsunduma yajin aiki —ASUU

ASUU ta ce za ta yanke hukunci tunda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika mata alkawari

Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta ce za ta dauki matakin da ya dace na da sa’a 48 masu zuwa kan Gwamnatin Tarayya saboda gazawar gwamnatin ta cika alkawuran da ta yi mata. 

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ne, ya bayyana haka a tattaunawarsa da Aminiya a ranar Litinin ta wayar tarho.

Shugaban kungiyar ya ce za su zartar da hukuncin da ya dace a ranar Talata tare da sanar da dukkanin sauran mambobinta matsayarta game da Gwamnatin Tarayya.

Idan ba a manta ba, a ranar 14 ga watan Oktoba ne ASUU da Ministan Kwadago, Chris Ngige suka gana tare da tattaunawa kan cika alkawuran da Gwamnatin Tarayya ta daukar musu.

Daga cikin matsalolin da suka tattauna akwai bukatar yih gyare-gyare a wasu jami’o’in kasar nan da kuma biyan alawus dain malamai.

Kazalika, an tattauna wasu alkawura da aka yi wa kungiyar tun a shekarar 2009 da kuma tsarin biyan albashin ma’aikata na IPPIS da kungiyar take adawa da shi.