✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ASUU: Sam gwamnatin Buhari ba ta muntunta Ilimi – Sanusi

Ya ce abin takaici ne yadda yajin aikin ASUU ya ki ci, ya ki cinyewa

Sarkin Kano na 14, Muhamadu Sunusi II, ya yi kakkausar suka ga gwamnati mai ci ta jam’iyyar APC da cewa sam ba ta martaba ilimi ba.

Sanusi ya yi wannan sukar ce a yayin jawabinsa a taron Majalisar Dinkin Duniya kan batun ilimi wanda aka yi a birnin New York na Amurka a makon da ya gabata.

Taron na kwanaki uku ya mayar da hankali ne kan neman mafita domin sauya ilimi daga tushe domin ci gaba.

Sanusi, wanda kuma shi ne Kalifan darikar Tijjaniyya a Najeriya ya ce gwamnatin APC karkashin Shugaban Kasa Muhammdu Buhari ba ta martaba ilimin ne ganin yadda ta ke tafiyar da batun yajin aikin malaman jami’o’i, wanda hakan ya sa aka rufe jami’oi tun watan Fabrairu.

“Abin da ke faruwa shi ne an yi rashin sa’ar samun wadanda ba sa martaba ilimi da kuma ba shi muhimmanci a madafun iko, wanda hakan ya sa ba a ganin girman [ilimi da kuma] malamai”.

“Yawancin malaman nan na da zabin aikin yi, amma suka zabi su ilimantar da ‘ya’yanmmu saboda su taimaka wa al’umma,”  inji Kalifan.

Sanusi ya kuma koka da yadda ake tafiyar da tsarin ilimi da albashi da kuma walwalar malamai baki daya, yana mai cewa abin takaici ne da ke bukatar gyara.