✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ASUU ta bukaci gwamnati ta kawo karshen matsalar tsaro

Kungiyar malaman Jami’o’i a Najeriya (ASUU), ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ba wa makaratun da ke fadin kasar nan kariya daga hare-haren…

Kungiyar malaman Jami’o’i a Najeriya (ASUU), ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ba wa makaratun da ke fadin kasar nan kariya daga hare-haren ‘yan ta’adda.

Shugaban kungiyar ASUU reshen Jami’ar harkokin noma ta gwamnatin tarayya da ke Makurdi (FUAM), Dokta Simon Ejembi, ya ce kiran ya zama wajibi saboda yadda ake samun karuwar hare-haren ‘yan bindiga da sauran kalubale na matsalar tsaro da ake fuskanta.

Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu daliban jami’ar FUAM yayin da suke neman ilimi domin samun kyakkyawar makoma a rayuwa.

“Kungiyar reshen Jami’ar ASUU-FUAM, ta yi Allah-wadai da kai hari da garkuwa da aka yi baya-bayan nan kan dalibanmu.

“Muna kiran gwamnati da sauran hukumomin tsaro da su kubutar da kasar nan daga halin da take ciki na tabarbarewar tsaro saboda mu tsira da kasarmu,” a cewar Dokta Simon.