✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ASUU ta yi watsi da tayin karin albashin malaman jami’a

Farfesa Osodeke ya ce sabon tayin karin albashin da gwamnati ta yi ba shi da amfani tunda ba a kansa suka yi yarjejeniya ba. 

Kungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya (ASUU) ta yi watsi da tayin Gwamnatin Tarayya ta yi musu na karin kashi 35 cikin 100 ga albashin furofesoshi da kuma kashi 23.5 ga sauran malamai da ma’aikatan jami’a.

Shugaban ASUU na Kasa, Farfesa Emmanuel Esodeke ya yi fatali da tayin ne, bayan Gwamnati ta shaida wa kungiyar cewa iya kason albashin da za ta iya kara musu ke nan.

“Muna magana ne game da adadin da aka yi cim-ma yarjejeniya, ba kason da aka yi mana tayi ba, ”in ji shi.

Farfesa Osodeke ya ce sabon tayin karin albashin da gwamnati ta yi ba shi da amfani tunda ba a kansa suka yi yarjejeniya ba.

Ya kuma yi zargin cewa tayin karin albashin gasar zare ne domin goga wa ASUU kashin kaji.

Wannan sabuwar dambarwa ta Kunno kai ne bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gargadi jami’an gwamanti kan sanya hannu a kan duk wata yarjejeniya ko alkawari da gwamnati ba ta iya cika wa ASUU ba.

Buhari ya kuma umarci wakilan Gwamnatin Tarayya da ke da ke tattaunawa da malaman jami’an da su yi kokarin shawo kansu su janye yajin aiki da suke gudanarwa.

Ministan Ilimi, ya bayyana wannan ne a taron da suka yi da iyayen jami’o’i da shugabannin jami’o’in Gwamnatin Tarayya a Abuja domin kawo karshen yajin aikin na ASUU.

Adamu ya bayyana musu cewa bayan ganawar Buhari da shi ministar kudi da na kwadago da Ministan Sadarwa Isa Pantami, da shugaban ofishin tsara albashi na kasa, sun gano cewa gwamnati ba za ta iya aiwatar karin albashin da aka bukata a rahoton Kwamitin Nuni Brigss da ya sake zama ka bukatun ASUU ba.

Sai dai ya yi alkawarin cewa daga  yanzu jami’o’in za su rika biyan sauran hakkokin duk wani karin aiki da malamai da ma’aikata suka yi a kan lokaci ga duk wanda ya yi aikin.

Ya kuma yi musu alkawarin Naira biliyan 150 a kasafin 2023, wanda ya kunshi Naira biliyan 100 na gyare-gyare da samar da kayan aiki a jami’o’in; da kuma biliyan 50 domin biyan bashin hakkokin malamai.

Adamu ya bayyana cewa yanayin tattalin arziki ne ya sa gwamnati ba za ta iya biyan duk bukatun malaman ba.

Don haka ya bukaci fahimta daga gare su domin janye yajin aikin da ya sa aka rufe jami’o’i na sama da kwana 200.

Ku bar karin albashin ku cika alkawari —ASUU ga gwamnati

Da yake mayar da martani kan sanarwar karin albashin, Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, a wata tattaunawa da Aminiya, ya bukaci gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma.

Ya yi zargin rashin gaskiya a tayin da Gwamnatin Tarayya ta yi, yana mai cewa wani yunkuri  ne na goga wa ’ya’yan kungiyar kashin kaji.

“Ba mu magana game da kason da za a kara, muna magana ne game da yarjejeniyar.

“Nawa suka gabatar mana da za su ba wa malamai a lokacin tattaunawa? Kamar yadda muka dage, ba ma karbar kyauta, kudin da aka yi yarjejeniya a kai muke so.

“Idan kyauta kuka ba mu, za ku iya janyewa gobe, amma idan muka yi yarjejeniya muka sanya hannu a kai, hakan ya shafi bangarorin biyu.

“Muna magana ne game da adadin da aka yi cim-ma yarjejeniya, ba kason da aka yi mana tayi ba, ”in ji shi.

Da aka nemi ya bayyana adadin kudin da aka tattauna, Osodeke ya ce, “Kada ku damu, ai ba su gama ba, idan sun gama duniya za ta sani.

“Idan ana tattaunawa ba a sanarwa har sai kun gama. Shi ya sa muke inda muke a yau

“Sun je sun gaya wa ’yan jarida domin su yi kokarin bata kungiyar kwadagon; matsalar ke nan.

“Idan da sun zauna suka bi ka’idojin yarjejeniyar, ba za mu kai inda muke a yau ba.”

Ya fayyace cewa daga yanzu kungiyar da kuma gwamnati sun kammala tattaunawar hadin gwiwa, yana mai cewa ya rage kawai sanya hannu.

“Mun kammala. Ya kamata su koma su dawo su sa hannu. Za mu bayyana lokacin da komai ya kare kuma mu sa hannu. ”