Atiku: Ruwa ba sa’an kwando ba ne – Sakon PDP ga Tinubu | Aminiya

Atiku: Ruwa ba sa’an kwando ba ne – Sakon PDP ga Tinubu

Tinubu da Atiku
Tinubu da Atiku
    Sani Ibrahim Paki

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce bai kamata dan takarar Shugaban Kasa na APC, Bola Ahmed Tinubu ya fara murna ba saboda ruwa ba sa’an kwando ba ne in kwatanta shi da nata, Atiku Abubakar.

A cewar PDP, Tinubu ya sami takarar ce a jam’iyyar da ta take gargarar mutuwa, wacce ta gaza cika ilahirin alkawuran da ta yi yakin neman zabe da su a baya.

Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar, Debo Ologunagba, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, jim kadan bayan an ayyana Tinubun a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwanin APC.

Sanarwar ta ce, “Muna tausaya wa Tinubu saboda wannan nasarar da ya samu, amma ya sani cewa ruwa fa ba sa’an kwando ba ne, Atiku ya fi shi shahara da cancanta da kuma shiri don zama Shugaban Najeriya.

“Nan ba da jimawa ba Tinubu zai gane Najeriya ba daya daga cikin wuraren da yake mulkin mallaka ba ce, kuma ’yan Najeriya ba yaransa ba ne, irin wadanda ya sayi tikitin takarar APC daga hannunsu.

“Kwanan nan zai fahimci cewa ’yan Najeriya ma haushinsa suke ji saboda yadda ya taimaka aka kakaba musu Buhari, wanda ya jefa rayuwarsu cikin kunci, talauci, zubar da jini, ta’addanci, kabilanci da bangaranci a kasarmu,” inji PDP.

Jam’iyyar ta kuma ce kalaman da Tinubun ya rika yi kafin zaben fid-da gwanin na nuni da yadda yake neman ya zama Shugaban Kasa ko ta wanne hali, domin ya sami damar yin facaka da baitil-malin kasar.