✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Atiku: Tinubu ya so yi min Mataimakin Shugaban Kasa amma na ki

Atiku ya ce ya ki amincewa Tinubu ya zame mishi dan takarar mataimakin shugaban kasa

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce jagoran Jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taba neman zame mishi dan takarar mataimakin shugaban kasa amma ya ce ba ya so.

Atiku ya bayyana cewa a kakar zaben 2007, lokacin da ya fara takarar shugaban kasa, Tinubu ya bijiro mishi da maganar, amma ya ki amincewa.

“A lokacin da na sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa AC wadda abokina Bola [Tinubu] ya kafa, ya shardanta min daukar shi a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa da sauran abubuwa kafin a ba ni takara.

“Amma na ce mishi a’a ba haka za a yi ba, maimakon in dauke shi a matsayin mataimakin shugaban kasa, na dauki Sanata Ben Obi,” inji Atiku.

Atiku ya bayyana haka ne a jawabinsa ga mambobin Kwamitin Amintattu na PDP ranar Talata, inda ya bukace su da kada su bari a tursasa wa jam’iyyar yarda da wani tsarin karba-karba gabanin zaben 2023.

Atiku, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2007, ya yi takara ne bayan sun raba gari da tsohon uban gidan nasa, wanda Atikun ke so ya gada a lokacin.

Bayan sun yi baram-baram, Atiku ya yi takarar shugaban kasa a jam’iyyar AC, wadda su Tinubu suka kafa, bayan guguwar siyasar da ta wuce da gwamnonin jam’iyyar AD da suka ci zabe a 1999.

Daga cikin gwamnonin AD da aka zaba a 1999 a yankin Kudu maso Yamma, Tinubu ne kadai ya kai bantensa a zaben 2003, bayan takun sakar da ta shiga tsakaninsu da Obasanjo ta yi waje-rod da sauran.

Gabanin karewar wa’adinsa na biyu a matsayin Gwamnan Jihar Legas, Tinubu ya kafa tubalin jam’iyyar AC, wadda a karkashinta aka zabi Ministan Ayyuka da Gidaje na yanzu, Babatunde Fashola, a matsayin magajin Tinubu a Jihar Legas.

A lokacin da Tinubu da Obasanjo suke wa juna kallon hadarin kaji ne Atiku ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP mai mulki zuwa AC, ya kuma samu tikitin takarar shugaban kasa.

Sai dai kuma bai kai labari ba, inda ya zo na uku a babban zaben 2007, wanda tsohon Shugaban Kasa, marigayi Umaru Musa Yar’Adua, ya lashe, Muhammadu Buhari na Jam’iyyar ANPP kuma ya zo na biyu.

Duk da haka AC ta samu kujeru 32 daga cikin kujeru 360 a Majalisar Wakilai da kujeru shida a Majalisar Dattawa mai kujeru 109.

Tsarin karba-karba

Atiku ya karyata abin da ya kira labarin kanzon kuregen da ake bazawa cewa yana shirya makarkashiya domin hana PDP bai wa yankin Kudu maso Gabas takarar shugaban kasa.

“Mun bullo da tsarin karba-karba ne a jam’iyyar nan da muka kafa saboda muna so kowane yankin kasar nan ya ji cewa ana damawa da shi, kuma daidai gwargwado, ni dai na yi nawa bangaren a kan batun karba-karba.

“Yawancinku ’yan PDP ne lokacin da gwamnoni suka shigo a 2003, suka nemi in tsaya takara amma na ce a’a, muka yi ittikafin cewa a bar wa Kudu maso Yamma, amma suka ce saboda me?

“Wasu daga cikin gwamnonin da suka goyi bayana har daure su an yi, wasu aka tsige su, amma duk da haka mun tababtar da wannan tsarin.

“Saboda haka babu yadda za a yi wani ya ce wa PDP ba ta bin tsarin karba-karba ko ga yadda za ta yi shi.

“A shekarun da PDP ta yi mulki shekara shida da shekara takwas duk yankin Kudu ne suka yi shugabanci. Saboda haka kada jam’iyyar adawa ta hana mu sakat. Su ne hakan ya wajaba a kansu, kuma ba su da zabi.

“Wasu na cewa ba a bai wa Kudu maso Yamma dama ba amma lokacin da na shiga jam’iyyar AC wadda abokina Bola (Tinubu) ya kafa, daga cikin sharudan zamana dan takarar shugaban kasa akwai batun daukar shi ya zama dan takarar mataimakin shugabna kasa.

“Amma na ce ‘a’a ba zan dauke ke a matsayin mataimakin shugaban kasa ba, maimakon haka zan dauki Sanata Ben Obi’,” inji Atiku.

Atiku ya kara da cewa da ya tashi fitowa a 2019 kuma sai ya dauki Peter Obi daga yankin Kudu Maso Gabas.

“Saboda haka babu wata hujja da suke da ita ta cewa ana neman mayar da yankin Kudu maso Gabas saniyar ware a tsarin karba-karba.

“Ina ga abu ne mai kyau mu fahimci cewa a matsayinmu na kusoshin siyasa babu wani abin da ake shiryawa da nuna wa wani yankin wariya,” inji Atiku.