✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Atiku ya kaddamar da takarar shugaban kasa ta zaben 2023

Ba ni da wata matsala a jam'iyyar PDP ko da sauran masu son fitowa takara.

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya kaddamar da takarar neman shugabancin kasar a babban zabe na 2023 mai zuwa a jam’iyyar adawa ta PDP.

Atiku, wanda ya shafe shekara fiye da 15 da suka wuce yana neman shugabancin Najeriya, ya ce zai mayar da hankali kan bangare biyar idan aka zabe shi a matsayin shugaban basa.

Da ya ke jawabi yayin taron wanda ya gudana Cibiyar Taro ta  International Conference Centre da ke Abuja a ranar Laraba, Atiku ya ce gwamnatinsa za ta zama gada tsakanin mulkin dattawa da na matasa.

“Gwamnatinmu za ta zama kamar gada ce [da za ta hada] tsakanin mulkin dattawa da na matasa.”

Ya ci gaba da cewa: “A karkashin mulkina, zan mayar da hankali kan bangare biyar masu muhimmanci; hadin kan Najeriya, tsaro, tattalin arziki, ilimi, ciyar da bangarorin gwamnatin tarayya gaba da kara musu iko.”

’Yan Najeriya ne ke son in yi takara a 2023 —Atiku

Atiku Abubakar, ya ce ’yan Najeriya ne ke son ya tsaya takarar shugaban kasa a babban zaben 2023.

Atiku ya sanar da haka ne ga manema labarai a Abuja, gabanin bayyana kudurinsa na neman takarar shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Ya bayyana cewa ba shi da wata matsala a jam’iyyar PDP ko da sauran masu son fitowa takara, domin kuwa idan suka zauna za su fitar da dan takara cikin ruwan sanyi.

“Idan muka shiga daki muka zauna za mu fitar da dan takara babu wata matsala,” a cewar Atiku.

Da yake magana kan matsalar tsaro a Najeriya, Atiku ya ce rashin zaman lafiya da kasar ke ciki abun takaici ne da ke bukatar a tashi tsaye a magance.

“Babu shakka akwai matsalolin rashin zaman lafiya kuma wadannan abubuwan sun faru ne saboda rashin shugabanci na gari,” a cewar Atiku.

Ya kuma soki yadda gwamnati mai ci ta bari tattalin arzikin Najeriya ya samu tawaya, wanda hakan ya jefa miliyoyin mutane cikin kuncin rayuwa.