✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Atiku ya ki daga hannun dan takarar Gwamna na PDP a Kano

Yana kaffa-kaffa ne saboda dakon hukuncin Kotun Koli

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a ranar Alhamis ya gudanar da gangamin yakin neman zabensa a Jihar Kano.

Kamar a sauran wurare, Atiku ya yi alkawarin sake bude iyakokin kasar nan, ya habaka harkokin noma da na kasuwanci da masana’antu, sannan ya samar da tsaro.

To sai dai babban abin da ya fi daukar hankali shi ne yadda dan takarar ya ki daga hannun dan takarar Gwamnan jam’iyyar, Alhaji Mohammed Sani Abacha.

Har yanzu dai mutum biyu ne ke ikirarin zama ’yan takarar tsakanin Mohammed Abachan da kuma Sadik Wali, amma Atiku ya ki ba kowa daga cikinsu tutar takarar jam’iyyar ko ya daga hannun wani a cikinsu.

Aminiya ta rawaito cewa tun bayan kammala zaben fid-da gwani, jam’iyyar take fama da rikici a Jihar, inda kowanne daga cikinsu yake cewa shi ne halastaccen dan takara.

Kazalika, wakilinmu ya lura cewa duka mutum biyun na tare da Atikun a filin wasa na Sani Abacha, inda aka gudanar da taron, amma tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya ki daga hannun kowa daga cikinsu yayin da yake jawabi.

Amma wata majiya a kusoshin jam’iyyar da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa wakilin namu cewa PDP na taka tsantsan ne saboda tana dakon hukuncin Kotun Koli a kan lamarin ranar Juma’a.

“Ba ma son Atiku ya daga hannun Abacha yau (Alhamis), gobe Juma’a kuma Kotun Koli ta ce Sadik ne dan takararmu,” in ji majiyar.

A takaitaccen jawabin da ya gabatar, Atiku ya tambayi Kanawa ko suna son zaman lafiya da habakar tattalin arziki da na masana’antu da na noma su dawo, inda suka amsa masa da eh.

Daga nan ne sai ya ce, “To gwamnatin PDP ce kadai za ta iya dawo da wadannan manufofin guda hudu. Shi ya sa nake rokonku da ku zabi PDP tun daga sama har kasa, ni kuma na yi muku alkawarin za mu aiwatar da su.”