✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Atiku ya taya Davido murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Ina taya ka murna ni da iyalinna da masoyanka kan zagayowar ranar haihuwarka mai cike da tarihi.

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya taya shahararren mawakin nan na Kudancin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Atiku ya taya Davido murnar ce cikin wani sako da ya wallafa a shafukansa na Facebook da Twitter.

“Ina taya ka murna ni da iyalina da masoyanka kan zagayowar ranar haihuwarka mai cike da tarihi,” a cewar sakon.

A cikin sakon da Waziri Adamawa ya wallafa a shafukansa, ya yi godiya a gare shi dangane da taimakon da Davidon zai bayar ga gidajen marayu na zunzurutun kudi har miliyan 250.

Bayanai sun ce a makon da ya gabata ne dai masoya da abokan arzikin mawakin suka tara masa miliyoyin kudi har Naira miliyan 200.

Aminiya ta ruwaito cewa, abokai da masoya sun tara wa Davido sama da Naira miliyan 100 a yini daya, inda daga bisani mawaki ya ce kudin sun kai naira miliyan 200.

Lamarin wanda aka fara cikin raha, ya zama abin magana a kafafen sadarwa.

Mawakin ne ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, “Muna samun daukaka ne idan muna taimakon wasu ko? To tunda na taimaka wajen daga wasu a shekaru da dama a baya, nima yanzu ina son ganin asalin abokaina. Dukan abokaina ina so su aiko min da Naira miliyan 1. An ce mu ne kungiyar Biliyan 30. Idan ba ka turo ba, ba ka cikinmu.”

Daga nan ne kuma ya kira abokan aikinsa su Mayorkun da Perruzzi da Dremo da Don Jazzy da sauransu.

Nan sai ya ajiye asusun ajiyan bankinsa, inda a cikin kankanin lokaci aka tara makudan kudade.

Daga cikin wadanda ya ce sun tura kudaden akwai Femi Otedola da Emeka Okonkwo da Obi Cubana da sauransu.

Davido zai raba N250m ga gidajen marayu a fadin Najeriya

Davido ya ce zai ba gidajen marayu da ke Najeriya zunzurutun kudi har naira miliyan 250, kwatankwacin dalar Amurka dubu dari 608, bayan da magoya bayansa suka tara masa Naira miliyan 200.

Kason da za a raba wa gidajen marayu ya hada da wanda magoya bayansa suka tura masa da kuma gudunmmawar naira miliyan hamsin kari da wani ya bayar.

Davido ya godewa wadanda suka ba da gudunmmawar kudi, yayin da ya bayyana yadda za a yi amfani da su.