✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Atiku zai gana da ’yan APC 1,615 da suka dawo PDP a Adamawa

Atiku ya bukaci gana wa da sabbin mambobin jam'iyyar a suka koma PDP.

Jam’iyyar PDP a Jihar Adamawa ta karbi mutum 1,615 da suka sauya sheka daga jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Toungo ta jihar.

Wadanda suka sauya sheka da ke zanga-zanga kan matsalar tsaro, sun bayyana karuwar tabarbarewar tsaro a matsayin gazawa da rashin cika alkawuran yakin neman zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Sun bayyana haka ne a wani biki da aka shirya a Toungo domin karbar su.

Tsofaffin ’yan jam’iyyar ta APC, irin su Mustapha Albishir, Malam Yahaya Abubakar, da Alhaji Gana da suka yi magana ta bakin wakilansu sun bayyana cewa talauci, tabarbarewar tattalin arziki, da rashin tsaro da ake fuskanta a gwamnatin Buhari ne ya sa suka fice daga jam’iyyar.

Sun ce sun yi nadamar shiga APC, domin a cewarsu, jam’iyyar ba ta samu ci gaba ba tun 2015, kuma a yanzu sun gamsu cewa PDP ce wurin da ya dace su zauna saboda sauye-sauyen da Gwamna Fintiri ya kawo lokacin da PDP ta karbi mulki a hannun APC a 2019.

“Tafiyarmu zuwa APC ba ta da amfani, mun hada kai don mu kayar da PDP a 2015 amma mun gane cewa mun yi kuskure.

“Daya daga cikin dalilan da ya sa sama da mutum 1,615 suka yanke shawarar zuwa nan a yau duk da cewa mun fi mutum 6,000 da ke son shiga PDP, shi ne saboda bayan shekara bakwai ba mu ga komai na zahiri da jam’iyyar ta samu a karkashin Buhari ba face tabarbarewar tsaro da talauci.

“Don haka ne muka yi kira ga ’ya’yanmu da ’yan uwa, da su sake yin taka-tsantsan domin ganin ci gaban da muka samu a Toungo.”

Yayin da yake karbar wadanda suka sauya sheka, Shugaban PDP na Jihar Adamawa, Barista Tahir Shehu ya ce tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, wanda dan gidan Sarautar ne, ya bukaci ya yi gana da mutum 1,615 da suka fice daga jam’iyyar wadanda suka nuna jajircewa wajen nuna kin amincewa da rashin shugabanci na gari.

“Ka’idar ita ce jam’iyyar ta karbi sauye-sauye a matakin unguwanni wanda jam’iyyar ta yi,” cewar Shehu.

“Atiku ya roki jam’iyyar da ta tabbatar da cewa mutum 1,615 da suka bar jam’iyyar daga Toungo sun halarci babban taron gangamin da za a yi a Yola a ranar 15 ga watan Agusta domin murnar ba shi tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, saboda yana son gaisawa da kowa”.