✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Atletico Madrid ta ci gaba da jan ragamar gasar Laliga

Atletico Madrid na da maki 41 daga wasanni 16 da ta buga a gasar Laliga ta bana.

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta ci gaba da jan ragamar gasar Laliga, bayan ta doke kungiyar Sevilla a daren ranar Talata.

Sevilla ta sha kashi ne a hannun Atletico Madrid da ci 2-0, ta hannun ’yan wasanta Angel Correa da kuma Saul Niguez.

Atletico Madrid na da maki 41 daga wasanni 16 da ta buga a gasar, inda ta ba wa Real Madrid tazarar maki 4 daga wasanni 18 da ta buga.

Kieran Trippier ya dawo buga wa Atletico Madrid wasa, bayan da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta dakatar da shi wassani 10, saboda karya ka’idojin caca.

Atletico Madrid na da damar kara ba da tazarar maki tsakaninta da Real Madrid, a yayin karawarta da Eibar a karshen wannan satin.

Real Madrid da Barcelona ba za su buga wasa a karshen wannan mako ba, saboda za su buga gasar Spanish Super Cup.