✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Atletico ta kama hanyar lashe gasar La Liga ta bana

Kungiyar ta tunkari cin kofin karo na 11 a tarihi.

Atletico Madrid ta dauko hanyar zama zakarar gasar La Liga ta bana bayan shafe shekaru bakwai ba tare da cin kofin ba.

Kungiyar ta tunkari cin kofin karo na 11 a tarihi, kuma nasararta za ta tabbata ne idan ta ci wasanni biyun da suka rage mata.

Wasanni biyu na gaba da ke tunkaro kungiyar su ne wanda za ta kara da Osasuna da Real Valladolid duk a cikin watan Mayun da muke ciki.

A yanzu kungiyar ta sake bayar da tazara tsakaninta da kungiyoyin Barcelona da Real Madrid da ke matakin na biyu da na uku wadanda suka shafe shekaru suna musayar lashe kofin a tsakaninsu.

Tazarar da kungiyar ta bayar na zuwa ne bayan nasarar da ta yi yayin haduwarta da Real Sociedad a ranar Laraba, inda tazarar da ke tsakaninta da Barcelona da ke mataki na biyu a teburin gasar ya zama maki hudu.