✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Atletico ta nada Fernando Torres kocin matasa

Ina alfahari da murna da na dawo gida.

Atletico Madrid ta nada tsohon dan wasanta, Fernando Torres a matsayin sabon kocin matasan kungiyar.

Torres ya sanar da hakan ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.

“Ina alfahari da murna da na dawo gida.

“Wannan kalubale ne babba a gaba na da zanyi iya kokari na don ci gaba da bautawa kungiyar nan.”

A kakar da ta gabata ce Torres ya yi aiki tare da karamar kungiyar Atletico a matamakin mataimakin koci, inda a yanzu zai ja ragamar kungiyar a kakar da za ta fafata ta bana.