✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Attahiru na daf da zama abin alfahari — Buratai

Tukur Buratai ya yi matukar kaduwa da rasuwar Janar Attahiru.

Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Tukur Buratai, ya ce marigayi Babban Hafsan Sojan Kasa yana gab da farantawa Najeriya rai kafin ajalinsa a iftila’in hadarin jirgin sama.

Buratai a cikin sakon ta’aziyyarsa ga marigayi Laftana-Janar Ibrahim Attahiru, ya ce yana samun gagarumin ci gaba a kan yaki da ayyukan ta’addanci da kokarin dakile sauran ayyukan tayar da kayar baya a daidai lokacin da ajali ya katse masa hanzari.

Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici ga dukkan ’yan Najeriya da masu son zaman lafiya, inda ya ce Attahiru da jami’an da suka mutu tare da shi manyan hafsoshi ne wadanda suka yi aiki yadda ya kamata.

“Yana gab da sanya al’ummar kasar yin alfahari a kan yakar ayyukan masu tayar da kayar baya da kuma kokarin magance ta’addanci lokacin da wannan lamarin ya faru.

“Ba na shakkar iyawarsa kamar yadda ya yi aiki a wurina a fannoni daban-daban kuma ya san makamar aikinsa da hadin gwiwar abokan aikinsa.

“Na yi matukar kaduwa da bakin ciki da labarin rasuwar magajina, Laftana-Janar Ibrahim Attahiru da mukaddashin Shugaban Hukumar Leken Asiri ta soji da mai rikon mukamin Provost Marshal a rundunar sojin kasa da shugaban ma’aikatansa da babban dogarinsa da mukaddashin mataimakin daraktan kudi a ofishinsa da mai bayar da umarni, da kuma matukan jirgin da ma’aikatan da ke cikin jirgin saman, a hadarin ranar 21 ga Mayu a filin jirgin sama na Kaduna.

“Ina so, a madadin iyalina, in sake jaddada ta’aziyyata ga Shugaban Kasa da Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Tarayyar Najeriya da iyalan mamatan da mai girma Ministan Tsaro da Shugaban Rundunonin Sojan Najeriya da Babban Hafsan Sojan sama da hazikan hafsoshi da sojojin kasa da sojojin sama na Najeriya a kan rasuwar wadannan jajirtattu kuma masu aminci da kishin kasa a lokacin da suke bakin aiki,” inji shi.

Buratai, ya bukaci sojojin da su rufe lamuransu tare da tabbatar da cewa abin da hafsoshin suka ci gaba da rayuwa ta hanyar karfafa nasarorin da aka samu a ayyukan daban-daban.

A cewarsa, sun sadaukar da rayukansu ne a cikin aiki da kuma kishin kasa ga kasa.

“Tunanina da addu’ata suna tare da iyalan wadannan manyan jarumai. Da fatan Allah Madaukakin Sarki Ya sa sun huta ke nan,” inji Buratai.