Auren Bakano da Ba’amurkiya: Bukatar a yi taka-tsantsan | Aminiya

Auren Bakano da Ba’amurkiya: Bukatar a yi taka-tsantsan

     BALARABE LADAN

A makon jiya ne wata Ba’amurkiya mai suna Jeanine Deisky  ta taso tun daga kasar Amurka ta iso Najerya da nufin ganawa da wani yaro saurayinta mai suna Suleiman Isa domin ta aure shi.

Ita dai wannnan Ba’amurkiya Jeanine, ta hadu da saurayin nata Suleiman ne ta hanyar kafar sada zumunta ta ‘Istagram’ inda suka rika tattaunawa har ta kai ga suna musayar hotunansu, daga bisani ita Jeanine ta amince  ta biyo matashi Suleiman zuwa Kano domin a daura masu aure.

Wannan Ba’amurkiyar mai shekara 46, an ce tana da ’ya’ya biyu kuma tana aiki ne a wani wurin sayar da abinci mai suna ‘Afghan Restaurant’ da ke Jihar Kalifoniya ta kasar Amurka.

Lokacin da ta iso Najeriya ta sauka a Kano ta gana da iyayen Suleiman, kuma labarin zuwanta Kano ya yadu ne saboda mahaifiyar yaron ta bayyana amincewarta da auren Suleiman da Jeanine, kuma har ta yarda ta dauki angon nata su tafi kasar Amurka bayan an daura auren.

Tun daga wannan lokaci ne labarin soyayyar Suleiman da Jeanine ya watsu kamar wutar daji, inda mutane kowa ke ta bayyana albarkacin bakinsa, wadansu na goyon bayan shirin, wadansu kuma suna suka.

Sai dai kuma mahaifin saurayi Suleiman mai suna Malam Isa, wanda tsohon dan sanda ne, ya ce ba zai amince da maganar auren ba sai ya sanar da jami’an tsaron cikin gida, (SSS) da nufin samun shawara daga gare su.

Haka kuma mahaifin yaron ya gindaya wa amarya Jeanine wasu ka’idoji wadanda suka hada da cewa lallai za ta bar dansa ya ci gaba da addininsa na Musulunci kuma za ta kyale shi ya ci gaba da karatunsa a can kasar Amurka, sharuddan da aka ce Jeanine ta amince da su.

Babu shakka akwai bukatar a yi taka-tsantsan kada a yi gaggawa, akwai bukatar a gudanar da bincike sosai, domin Suleiman yaro ne matashi dan shekara 23, ita kuma cikakkiyar mace ce ’yar shekara 46, wato ta ninka shekarunsa, saboda haka ta fi shi wayo da sanin inda duniya ta dosa. Kuma a wurinta ne zai zauna a kasar Amurka, bai san kowa ba sai ita, ita ce cinsa da wurin kwanansa da komai yake bukata na rayuwa, domin haka sai yadda ta yi da shi.

Abin tsoro shi ne an ce wannan mata tana da ’ya’ya biyu, shin ta taba yin aure ne ta same su ko kuwa ta same su ne ba tare da aure ba, kuma wane tabbaci ake da shi cewa ba za ta mayar da Suleiman mijin nata yaron gida ba?

Domin gudun kada a yi da-na-sani,  lallai ne a yi bincike mai zurfi kafin a daura auren. Ya yi kyau da aka ce za a bincika domin sanin ko wace ce Jeanine kuma ko ’yan uwanta, wato waliyanta sun amince a yi auren.

Akwai kungiyar ’yan Arewa mazauna kasar Amurka mai suna Zumunta, ya kamata a nemi shawararsu kafin a daura auren, Shugaban Sashin Hausa na Muryar Amurka Aliyu Mustapha Sakkwato jigo ne a kungiyar, za a iya tuntubarsa domin samun shawara, saboda ya dade a kasar Amurka.

Akwai mutane da dama da za a iya tuntuba domin tabbatar da cewa ba a yi kitso da kwarkwata ba, kamar Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Amurka da Ofishin Jakadancin Amurka da ke Najeriya don su san halin da ake ciki.

Haka kuma akwai wata ’yar Kano da ta auri wani Ba’amurke a watan Yunin 2018, wacce ita ma ta hanyar kafar sadarwa ta hadu da shi, inda bayan sun kwashe shekara biyu suna soyayya ya biyo ta Kano ya Musulunta aka daura masu aure suka koma kasar Amurka da zama. Idan da hali ana iya tuntubarta domin ta bayar da shawara, domin ita yanzu ta fahimci wasu abubuwa da suka taso bayan auren nasu.

Lallai a daure a yi bincike, kada a bi na yaro Suleiman, domin Hausawa sun ce ‘ta yaro kyau gare ta, ba ta karko.’ Shi yanzu ya fada kogin soyayya, idonsa ya rufe, saboda haka yana bukatar a taimaka masa don kada ya fada cikin hallaka, domin akwai aure irin wannan da dama da aka yi sakamakon haduwa ta hanyar kafar sadarwa amma ba a dade ba aka rabu baram-baram. Wadanda irin auren ya kai su wasu kasashen  su ne suka fi ganin tasku, domin da kyar suke kwatar kawunansu su dawo gida Najeriya. Allah dai Ya tabbatar da alheri.