✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Auren Mata dubu: An daure malami shekara dubu a Turkiyya

Wata kotun kasar Turkiyya ta daure wani malami mai suna Adnan Oktar sama da shekara dubu a kurkuku bayan kama shi tare da wadansu mutum…

Wata kotun kasar Turkiyya ta daure wani malami mai suna Adnan Oktar sama da shekara dubu a kurkuku bayan kama shi tare da wadansu mutum 200 da ake zargi da cin zarafin mata.

An kama mutumin wanda ya dauki kansa a matsayin malami da ake zargi kewaye da matan da ke shigar bayyana tsaraici kuma yake kiransu ’ya’yan kyanwa.

An tuhumi Adnan Oktar da auren mata dubu da kuma yada da’awar bautar halittu da addinin gargajiya yayin da matan ke zagaye da shi cikin tsiraici.

Hukumomin Turkiyya sun ce mafi yawan matan da suke tare da shi an yi musu sauyin halitta ne daga maza zuwa mata ta hanyar yi musu tiyata.

An kama su ne suna rawa a zagaye da shi bayan an sanya musu kida a dakin da ake kirkirar sauti na wani gidan talabijin dinsa.

Adnan Oktar mai shekara 64 wanda aka tsare tun a 2018 tare da wadansu da ake zargin masu aikata laifi ne, ’yan sandan Instanbul sashen binciken masu aikata laifukan da suke da alaka da kudi ne suka kama su.

An yanke wa Adnan Oktar daurin shekara 1,075 sakamakon laifukan da suka hada da cin zarafin mata da kananan yara da damfara da shiga rigar siyasa ko ta jami’an soji.

Kamar yadda jaridar NTV ta ruwaito, kotun ta kuma yanke wa wadansu manyan jami’an kamfanin Oktar da suka hada da Tarkan Yabas daurin shekara 211 da Oktar Babuna shekara 186.

Kazalika, Kamfanin Dillancin Labarai na Anadolu ya ruwaito cewa, an samu Oktar da karin laifuka na taimakon wata kungiya ta dan asalin Turkiyya mazaunin Amurka, Fethullah Gulen wanda kasar Turkiyya take zargi da yunkurin juyin mulki a shekarar 2016.

Sai dai Adnan ya musanta alakarsa da Gulen, sannan ya yi martani kan zargin cewa yana da kungiyar matsafa da take kunshe da mata, inda ya ce “wannan bakon abu ne ban san da shi ba.”

Majiyar Anadolu ta ruwaito cewa mutum 236 da ke kare Adnan za a ci gaba da tuhumarsu, yayin da za a ci gaba da tsare mutum 78 har zuwa lokacin zartar musu da hukunci.

Adnan Oktar ya bayyana wa alkalin kotun cewa a watan Disambar 2018 yana da budurwa da sun kai kusan dubu da yake tarayya da su.

Yayin sauraron kararsa a watan Oktoban bara ne Oktar ya bayyana cewa, “kaunar mata ta yi kane-kane a zuciya ta, kuma so da kaunar mace dabi’a ce ta kowane mutum kuma hakan take ga musulmi.”

A wani lokaci na daban, Oktar ya ce, yana da karfin sha’awa da lafiyar mazakuta mai tsananin gaske.