✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Auren ‘Wuf’ ba shi da wata illa a Musulunci – Sheik Daurawa

Malamin ya ce babu wata illa a Musulunce ko a likitance, ko a al’adance.

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Kano, Sheik Aminu Ibrahim Daurawa ya ce babu wata illa a auren ‘Wuf’ tsakanin masoya.

Malamin, wanda ya tabbatar da hakan a wai sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi.

Galibi dai ana amfani da kalmar ne a kan namijin da ya auri matar da ta fi shi yawan shekaru, musamman ma in tana da hannu da shuni, ko kuma namiji ya auri matar da ya girma sosai sai a ce ya yi ‘caraf’ da ita.

A cewar Sheik Daurawa, wanda tsohon shugaban hukumar Hisbah ne ta Jihar Kano, ko a addinnance babu laifi mace tayi wuf da saurayin da ta girma, ko kuma namiji yayi wuf da matar da ya girma.

Malamin ya kawo dalilai a bangaren al’ada da addini da kuma lafiya, inda duk ya tabbatar da cewa babu wani kwakkwaran dalili da ya hana yin hakan.

Ya ce, “A addini babu laifi ayi aure tare da bambancin shekaru idan kowa daga ciki ya gamsu, mace tafi miji shekaru, ko shi ya fi ta shekaru babu wata matsala a addini, musamman idan an duba wata masalaha.

“Ta bangaran al’ada ma babu matsala domin surutu ne ake yi saboda ba a fiye samun haka ba, musamman ta bangaran matan, saboda wasu suna ga kamar an yiwa saurayi wayo idan ya auri babba ko kuma ace kwadayi ya kai shi,” inji Sheik Daurawa.