Australiya na neman tsare Djokovic | Aminiya

Australiya na neman tsare Djokovic

    Sagir Kano Saleh

Gwamnatin kasar Australiya na yunkurin tsare gwarzon dan wasan kwallon tennis na duniya, Novak Djokovic, a ranar Asabar zuwa ranar Asabar.

Wani lauya gwamnati, Barista Stephen Lloyd ya shaida wa wani zaman gaggawa da kotu ta yi a ranar Juma’a cewa Gwamnatin Australiya na bukatar haka ne bayan ta soke takardar izininsa ta shiga kasar a karo na iyu.

Hakan na nufin za a tsare gwarzon dan wasan kwallon tennisn na duniya, in ba haka, sai dai ya halarci zaman kotun ta intanet daga ofishin lauyansa tare da jami’an shige da fice.