✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muhimman abubuwa a lokacin Babbar Sallah

Abubuwan da ya kamata a rika yi a lokacin Babbar Sallah

Muna taya ku farin ciki da Allah Ya sa muka shaida zagayowar Babba Sallah.

Saboda haka muka yi muku guzurin wasu abubuwa da ya kamata a lizimta a lokacin nan, a takaice:

 • Kabbarori.
 • Jinkirta cin abinci
 • Wankan ranar idi
 • Sanya turare
 • Caba ado
 • Sanya kaya masu launi
 • Halartar sallar idi
 • Babu nafila kafin sallar idi
 • Sauraron hudubar idi
 • Sauya hanyar komawa gida
 • Yanka dabbar layya bayan liman
 • Bude baki naman layya
 • Taya juna murna
 • Ba a azumi a ranar sallah
 • Ayyukan alheri

Duk da yake wadannan abubuwa kan zo a duk shekara, yana da kyau a dan yi karin haske game da su.

 • Kabbarori: Ana so a rika yin kabbarori, musamman bayan sallolin farilla daga sallar asuba ta ranar idi, har a yi sallolin farilla 20.

Kabbarar ita ce: Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar, La ilaha illal Lahu, Allahu Akbar Allahu Akbar walil Lahula hamdu.

 • Wankar idi: Daga cikin ladubban ranar idi akwai yin wankan ibada. Wankan tsarki mutum zai yi domin dacewa da hakan.
 • Jinkirta cin abinci: A babbar sallah ana so mutum ya kame baki kar ya ci komai har sai an sauko daga sallar idi.

Idan mutum zai yi layya an fi son abun da zai fara ci ya zama naman dabbar layyar da ya yanka.

 • Sanya turare: Ana so Musulmi ya fesa turare bayan ya yi wanka a ranar idi domin ya fita yana kanshi.

Amma kuma ba a so mace ta sanya turare idan za ta shiga cikin jama’a.

 • Caba ado: Ranar idi rana ce ado da kwalliyya, shi ya sa ake bukatar Musulmi ya sanya sabbin kaya a ranar, ga mai halin yin haka.

Kayan su kasance kyawawa, wadanda mutum ya fi so, kuma su kasance da tsafta.

Amma mata, ana bukatar su rufe kwalliyarsu da adonsu daga wadanda ba muharramansu ba.

 • Tufafi masu launi: Yayin da ake son sanya fararen kaya a ranar Juma’a, da sallah kuma ana so ne mutum ya sa kaya masu wani kala, ba farare ba.
 • Halartar sallar idi: Maza da mata, manya da kanana da ma masu jinin al’ada ana so su halarci hawan idi.

A kokarta a fita sallar idi da wuri saboda a samu a kintsa kafin isowar liman.

Mata za su kasance ne a bayan sahun maza, su kuma masu jinin al’ada za su ware gefe , sai an kammala sallar.

 • Ba a yin nafila kafin sallar idi: Da an je sai a samu wuri a zauna a jira isowar liman kafin a tayar da Sallah.
 • Sauraron huduba: Bayan idar da sallar idi, sai a jira a saurari hudubar liman cikin natsuwa.

Kuskure ne babba mutum ya yi magana a lokacin da limami ke yin huduba.

Bayan liman ya kammala huduba, idan yana da halin yin layya  yakan yanka dabbar layyarsa a gaban jama’a domin su ma su je su yanka nasu.

Idan kuma ba shi da hali sai ya sanar, ya kuma ba da izinin kowa ya je ya yanka nasa.

 • Sauya hanyar: Abun da ake so shi ne idan mutum zai koma gida sai ya bi ta wata hanya sabanin wacce ya bi a lokacin da zai je filin idi.
 • Yanka dabbar layya: Akan fara yanka dabbar layya ce bayan limamin unguwar da yin layyan yake ya fara yankawa.

Mai yin layya ko da mace ce, shi ake so ya yanka dabbarsa, amma ana wakilci.

Sai dai duk wanda ya yanka dabbarsa kafin liman to layyarsa ba ta yi ba.

Mazauna yankunan da babu masallacin idi kuma, za su iya yanka dabbobinsu bayan sun samu labarin cewa limami ya yanka, ko kuma bayan hatsi.

Ana dakatar da yanka dabbar ne idan magariba ta yi.

Washegarin ranar idi, har zuwa kwana uku bayan ranar idi duk za a iya ci gaba da yin layya daga hantsi har zuwa Magariba.

 • Bude baki da naman layya: Ga wanda ya yi layya an fi so abin da zai fara ci a ranar babbar Sallah ya kasance daga naman dabbar layyar.
 • Yi wa juna murna: A ranakun sallah ana so Musulmai su rika taya juna murnar arzikin ganin lokacin da kuma addu’o’i na alheri.
 • Ba a azumi a ranakun yanka: Ranar sallah rana ce ta ci da sha kuma Allah na fushi da duk wanda ke yin azumi a ranar idi.

Kazalika ba a yin azumi a ranakun layya, wato kwanaki uku da ke biye da ranar babbar sallah.

 • Ayyukan alheri: A yawaita bayar da kyauta, musamman ga mabukata da kananan yara. A sadar da zumunci, a kai ziyara sannan a gode wa Allah da Ya sa muka ga sallar.

Mulahaza:

Tabbatar da cewa kana sanye da takunkumin COVID-19 tare da kiyaye matakan kariya a kowane lokaci, muddin za ka shiga cikin jama’a.

A kiyaye dokokin hanya da na sauran hukumomi a ko yaushe.

A rika lura da kananan yara a kuma ba wa jami’an tsaro hadin kai.

Yadda wasu ’yan kabilar Ibo ke shirin Babbar Sallah

Yadda ake bikin sallah a gidan Babban Limamin Imo, Shaikh Suleiman Yusuf Njoku

Kamar sauran Musulmai a fadin duniya, iyalan Alhaji Suleiman Njokwu, na shirye-shiryen bikin Babba Sallah.

A idin babbar sallah ana bukatar Musulmai masu hali su yanka dabbar layya.

A matsayinsa na Babban Limamin Jihar Imo, Imam Suleiman Njokwu na da karin nauyi a kansa n ilmantarwa da kuma fahimtar da Musulmi a fadin  jihar wanda kuma ke bukatar sa ya yi kyakkyawan shiri.

Sai dai bana idin ya sha bamban, domin maimakon yadda aka saba yin sallar a filin idi da ke Nekede ko Amausa, bana za a yi  sallar ce a cikin masallatai saboda annobar coronavirus.

“Za mu yi sallar a cikin masallatai, bisa tsarin dokar COVID-19, musamman na bayar da tazara da kuma sanya takunkumi”, inji shi.

Bukukuwan da aka yi a baya

Amma a baya ba haka aka saba yin sallar Idin ba.

“Lokacin idi akan yi shagulgula ne da kuma kawa”, akan yi “bukukuwa da ciye-ciye da tande-tande iri-iri har a raba wa mutane a kuma ziyarci abokan arziki.

“Yanzu wannan ya kau. Dole mu san yadda za mu yi bikin ta yadda ba za mu saba dokar COVID-19 ba.

Wannan shekarar ba za a yi shagulgula ba.

A matsayinsa na limami

Kasancewrsa mai mata daya da ‘ya’ya uku, yawan iyalansa bai kai na mahaifinsa ba, Alhaji Yusuf Njoku, mai mata uku da ‘ya’ya 14, wanda ya rasu a 1995.

Mahaifin nasa ya zauna a Kano inda ya auri matarsa ta farko, wadda Bafulatana ce.

Mahaifiyar Imam Suleiman Njoku, ‘yar asalin Umuevu Umuokrika da ke Mbaise a Jihar ta Imo ita ce matar mahaifinsa ta biyu.

A shekarar da ta gabata ne Majalisar Musulmai ta Jihar Imo ta nada Babban Limamin Jihar, bayan rasuwar Alhaji Dauda Onyeagocha.

Bayan jagorancin sallolin Juma’a da na ido, Imam Njoku kan shirya liyafar sallah a gida.

Bikin sallah a cikin gida

Bayan hawan idi Imam Njoku da iyalansa kan koma gida ne tare da ‘yan uwa inda suke shakatawa da kuma karbar bakuncin masu kawo musu ziyara.

Amma ya ce, “hatta Shugaba Buhari ya hana [mutane] su kai masa ziyara a Aso Rock a lokacin [karamar Sallah].

“Saboda haka sai mu yi bikin ba tare da yin taro ba, saboda yanayin da muke ciki”, inji shi.

Ya ce, “A matsayinmu na iyali, insha Allahu za mu yi bikin daidai da dokar Allah. Manufar ita ce nuna farin ciki da gode wa Allah da Ya raya mu zuwa wannan lokaci”.

‘Gwamnati ta san na yi da tsoffin ‘yan Boko Haram’

Sanata Ali Ndume ya ce a ana wahalar da kai ne kawai a kan 'yan Boko Haram masu tubar muzuru

Sanata Ali Ndume (APC, Borno ta kudu) ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bar bata lokacinta wajen saita tunanin ‘yan Boko Haram saboda a cewarsa ba za su taba tuba ba.

Ndume, ya ce da yawa daga cikin wadanda gwamnati ta saita tunaninsu ta kuma maido su cikin al’umma sun koma kashe-kashensu.

A hirar da BBC Hausa ta yi da shi, dan Majalisar Dattawan ya ce, “Mafi yawa daga cikinsu da suka fito sun koma. Ba za su taba gyaruwa ba. Gwamnati ta san yadda za ta yi da su.

“Wadannan mutane ne kamar khawarijawa (baudaddu). Gwamnati ta san yadda za ta yi da su amma ba dai a kawo wa mutum wanda ya kashe mar mahaifi ko dan’uwa ba.

“Kuma ba wai ya tubar maka ba ne, gwamnati ya tubar mawa. Yana ganin kamar gwamnati ce ta kasa shi yasa ta lallabe shi ya dawo cikinsu”.

Ndume ya ce jama’arsu ba su gamsu da shirin na gwamnati ba don haka “ya kamata a dakatar da shi”.

“Idan da gaske ake yin wannan abun to wadanda suke sansanin gudun hijira ya kamata a koya wa sana’o’i don su taimaki rayuwarsu”, inji Ndume.

A halin yanzu, Gwamnatin Tarayya ta yaye tsofaffin ‘yan Boko haram 600 a shirin nata da sojin kasa suka kirkira a karashi shirin Operation Safe Corridor, a shekarar 2016.

Makasudin kirkirarar sa shi ne saita tunanin ‘yan Boko haram din da kuma sake mayar sa su cikin al’umma.

Shirin dai ya fuskanci kalubale musamman daga mutanen da ‘yan kungiyar suka kashe musu iyaye da yan’uwa ko mata da aka kashe musu mazaje aka bar su da marayu.

Daniel Shagah ya zama Sarkin Bachama

An nada Dakta Daniel Ismaila Shagah a matsayin sabon Hamma Bachama, wato sarkin Bachama da ke jihar Adamawa. Mai magana da yawun Gwamna Ahmadu Fintiri…

An nada Dakta Daniel Ismaila Shagah a matsayin sabon Hamma Bachama, wato sarkin Bachama da ke jihar Adamawa.

Mai magana da yawun Gwamna Ahmadu Fintiri ya fitar, a ranar Laraba, ya ce masu zabar Sarki sun zabi Daniel ya maye gurbi Sarkin da ya rasu a watan jiya, Stephen Honest Irmiya

“Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya aminta da zabar Dakta Daniel Ismaila Shagah a matsayin sabon Hamma Bachama bayan rasuwar sarki na 28 a Masarautar Bachama, Honest Irmiya Stephen, wanda ya rasu ciki watan jiya.

“Gwamna Ahmadu Fintiri na taya sabon sarki murna da kuma jinjina ga masu zabar sarkin saboda yadda suka gudanar da zaben Dakta Shagah cikin lumana,” kamar yadda takardar ta ce.

Ya kuma hori sabon sarkin da ya ci gaba abubuwa na gari da ya tarar tsohon sarkin ya yi.

Gwaman ya kuma bukace shi ya yi amfani da iliminshi wajen ciyar da al’umma gaba.

Ya ce, a matsayin sabon sarki na tsohon ma’aikacin gwamnati, yana da yakinin zai kula da mutanensa, musamman ta fannin samar da zaman lafiya.

“Ina da tabbacin zai dora bisa kyawawan ayyukan da marigayi Honest Stephen ya yi tsayin daka musamman a kan samar da hanyoyin zaman lafiya.

Ya Kuma roki masarautar da ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiyar da aka san ta da shi da kuma al’adu kyawawa.

Dalilan Najeriya na ba wa Nijar wutar lantarki

Kasashen Nijar da Benin da Togo na samun wutar lantarki daga Najeriya

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana dalilin da ya sa Najeriya take sayar wa kasashen Nijar da Benin da Togo wutar lantarki.

Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya ce ana sayar wa da kasashen wutar ne bisa yarjejeniyar cewar ba za su datse ruwan da yake shigowa Najeriya yake kuma samar wa manyan madatsun ruwata na Kainji, Jebba da kuma Shiroro karfin sarrafa wutar ba.

Garba Shehu ya ce, “Manufar yarjejeniyar da tasa muke ba su wutar ita ce cewa ba zasu gina madatsun ruwa a kan Kogin Naija ba, ita kuma Najeriya da sauran makwabtanta ba za ta yi hakan ba ga Kogin Nil da ya ratsa ta kasashen Itofiya, Sudan da Masar ba.

“Ya zuwa karshen shekara ta 2019, yawan bashin da ake bin wadannan kasashen guda uku ya kai Dala miliyan 69, ko da dai sun yi kokarin biyan kaso mai tsoka daga cikinsa.

“A yanzu haka kuma, ana bin kasashen Jamhuriyar Nijar da Benin bashin kudin wutar da ya kai Dala miliyan 16, kwatankwacin Naira biliyan daya da miliyan 200”, inji shi.

Kakakin Shugaban Kasar ya kara da cewa farashin wutar lantarkin da dukkannin kamfanoni suka samar a shekarun 2018 da 2019 a Najeriya ya haura Naira tiriliyan daya da biliyan 200.

Ya kuma ce kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 na Najeriya sun raba sama da kashi 90 cikin 100 na wautar da aka samar a kasar.

Miji ya kashe matarsa mai juna biyu

Wani magidanci dan shekara 47 ya gurfana a gaban kotu bisa zargin lakada wa matarsa mai juna biyu dukan tsiya har sai da ta mutu.…

Wani magidanci dan shekara 47 ya gurfana a gaban kotu bisa zargin lakada wa matarsa mai juna biyu dukan tsiya har sai da ta mutu.

Bayan dukan da mutumin ya yi wa matar tasa mai suna Blessing har ta mutu tare da abun da take dauke da shi ne aka gurfanar da shi a kotu.

Magidancin ya yi aika-aikan ne a cikin watan Afrilu a gidansu da ke kan titin Oke-Agba a birinin Akure.

Dan sanda mai shigar da kara Insfekta Uloh Goodluck ya shaida wa kotun cewa laifin ya saba wa sashe na 319, karamin sashe na daya na kundin manyan laifuffuka na jihar ta Ondo.

Ya kuma bukaci kotun da ta umarci a ci gaba da tsare mutumin har ya zuwa lokacin za a yanke masa hukunci la’akari da girman laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Lauyan wanda ake zargi, A. Ololike bai ja da bukatar dan sanda mai shigar da karar ba.

Daga nan ne kuma alkalin kotun, Mai Shari’a N. T. Aladejana ya umarci a ci gaba da tsare Mista Olabode har zuwa lokacin da za a yanke masa hukuncin.

Kotun da dage sauraron shari’ar zuwa ranar takwas ga watan Satumba mai kamawa.

Fasinjoji sun koka kan karin kudin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Ministan sufuri ya ce gwamnati ba za ta dauki asara ba, sai dai ina so ake ya rufe tashoshin

Fasinjoji sun koka kwarai kan karin kudin jirgin kasa da aka yi daga Abuja zuwa Kaduna.

Wakilinmu da ya ziyarci tashar jirgin kasa da ke Idu a Abuja, ya ce babu fasinjoji sosai saboda an ninka kudin tikitin jirgin.

Manajan gudanarwar hukumar jirgin kasa, Victor Adamu, ya ce juye biyu na fasinjoji farko da suka dauka mutum 679 ne.

“Da karfe bakwai na safe, daukar farko daga Idu zuwa Kaduna mun samu fasinja 396, sai tafiya ta biyu mun dauki fasinja 283.

“Daga Kaduna zuwa Abuja, dibar farko da karfe 8:45 na safe mun samu fasinja 94 sai a dauka ta biyu muka samu 75”, inji manajan.

Jirgin kasa ya dawo aiki ne ranar Laraba 28 ga Yuli, 2020 bisa tsarin bayar da tazarar da yin feshin magani don kariya daga COVID-19 wadda ta sa aka rufe tashoshin na tsawon watanni.

Gabanin bude tashoshin, Ministan Sufuri Rotimi a Amaechi ya sanar da ninka farashin tikiti tare da wajabta bin matakan kariya ga dukkanin fasinjoji.

‘Hawa jirgin zai gagari talaka’

Fasinjoji da suka hau jirgin baya dawo da jigilar sun koka kwarai da karin kudin jirgin inda wasu suka ce babu tausayi ciki.

Amma kuma sun yaba wa hukumar jirgin kasa wajen bin dokokin kariya na COVID-19.

Wata fasinja, Mairo Hassan ta ce karin da ka yi zai sa shiga jirgin ya gagari ‘yan Najeriya masu karamin karfi.

“Annobar COVID-19 ta karya tattalin arzikin mutane. Ka duba, mutane ba su cika ko tarago daya ba saboda tsadar jirgin.

“A da babu masaka tsinke idan ka zo nan. Ya kamata a duba dai”, a ganawarta da wakilinmu.

Jirgin zai gagari talaka

A nata ra’ayin, Zeenat Ahmed, cewa ta yi bai kamata gwamnati ta kara kudin jirgin haka ba.

“Maimakon a ninka kudin, kamata ya yi gwamnati ta biya rabi, fasinja su biya rabi.

“Kafin wannan lokacin, ina biyan N2,500 a taragon manyan mutane, amma yanzu sun mayar da shi N6,000.

“Ga shi kuma hanyar ba tsaro, fasinja za su so su biya ko nawa amma babu kudi yanzu”, inji ta.

‘Gwamnati ba za ta dauki asara ba’

Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi, a ziyarara ta ganin yadda ake bin kaidojin COVID-19 ya ce gwamnati ba za ta dauki asarar kujerun da ake tsallakewa ba a cikin jirgin don bayar da tazara.

“An samu karin kudin ne saboda a samu kudin tafiyar da harkar jirgin.

“Idan mutane ba sa so sai mu bari, amma dole ne a kara kudin jirgin in har ana so mu yi aiki.

“Abun da ya fi komai muhimmaci shi ne lafiyar mutum”, inji Amaechi.

‘Yan fashi sun kashe ‘yan sanda a motar kudi

‘Yan fashi sun kai wa motar daukar kudi hari suka kashe ‘yan sanda hudu da ke rakiyar kudin zuwa birnin Abakiliki, Jihar Ebonyi. Abun ya…

‘Yan fashi sun kai wa motar daukar kudi hari suka kashe ‘yan sanda hudu da ke rakiyar kudin zuwa birnin Abakiliki, Jihar Ebonyi.

Abun ya faru ne a mahadar hanya da ke garin Ezzemgbo na Karamar Hukumar Ohaukwu.

Wata majiya ta ce, ‘yan fashin sun tare motar ce a kan hanyarta na kai kudi wani banki da ke titin Ogoja a birnin Abakiliki.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Philip Maku ya tabbatar da cewar ‘yan fashin sun biyo motar ne daga Inugu.

Ya kara da cewa ‘yan fashin ba su dauki kudin ba saboda direban ya tsere musu.

“Sun fasa tayar motar daukar kudin daya amma direban ya tsere da motar da kudin. Sun kasa bin motar ne saboda driver ya tunkari sansanin sojoji”.

Kwamishinan ya ce, ‘yan sanda biyu da suka ji ciwo an kai su Asibiti. Sai kuma gawarwakinsu a mucuwari.

Ya kuma ce ‘yan sanda sun bazama nema ‘yan fashin.

Yadda ake hada-hadar ragunan layya a Najeriya

Farashin ragunan layya da yadda kasuwanninsu ke ci a sassan Najeriya

Yayin da Babbar Sallah ta matso sosai, hada-hadar raguna da sauran dabbobin layya ta kankama a sassan Najeriya.

Aminiya ta zagaya sassan kasar domin gano farashin raguna da yanayin hada-hadar dabbobin a kasuwanni daban-daban.

A akasarin jihohin da Aminiya ta ziyarta, masu sayar da raguna sun ce dabbobin sun yi tsada, in banda a wasu jihohin ‘yan kalilan.

Yawanci sun ta’allaka karancin sayen dabbobin da rashin kudi a hannun mutane wanda kullen COVID-19 ya haifar.

Kano babu ciniki sosai

A babbar kasuwar dabbobi ta ‘Yan-Awaki da ke Kano, Aminiya ta iske dabbobi jibge, ga kuma masu saye suna ta hada-hada.

Wani mai sayar da dabbobi a can, Malam Ali Ahmed, ya ce duk da karancin cinikin a bana sukan sayar da dabbobi kusan 1,000 a kullum.

“Mukan loda kimanin tirela bakwai zuwa takwas ta dabbobi a kullum a ‘yan kwanakin nan domin kaiwa wasu jihohin musamman na Kudancin Najeriya”, inji shi.

Yanayin farashi da hada-hada a kasuwannin dabbobin layya a Najeriya
Dubun dubatar raguna a kasuwar dabbobi a Kano

Game da farashin raguna a kasuwar, ya ce manyan kan kai N180,000 zuwa N200,000, matsakaita kuma N65,000 zuwa N75,000 sai kanana da ke kai kimanin N15,000.

Ya kara da cewa yawanci sukan sayo dabbobin ne daga jihohin Arewa maso Gabas da ma wani bangare na Jamhuriyar Nijar.

Mutane ba su da kudi

Wani mai sarin raguna yana kaiwa Kudancin Najeriya, Mohammed Sani Kofar Wambai ya ce ragon da suka saya dubu 40 a bara, bana baya wuce dubu 35.

“Ana ciniki sosai Alhamdulillah amma bara gaskiya an fi ciniki saboda rashin kudi a hannun mutane”.

A kasuwar dabbobi da ke Hotoro Tunshama kuwa, Malam Abdullahi Muhammad Kawon Kudu mai sayar da raguna ya ce sukan taba ciniki duk da karancin kudin da mutane ke yi a bana.

Kasuwar dabbobi ta ‘Yan Awaki a Kano

Shi kuwa wani mai sayen rago a kasuwar ta Tunshama, Malam Halilu Ahmad ya ce bara raguna biyu ya yanka, amma bana guda daya zai yi layyar.

“Akwai makwabtana da suke yankawa duk shekara amma bana sun yanke shawarar kawai su hada kudi su sayi sa su yanka su yi watanda saboda ba za su iya sayen ragunan ba duk kuwa da cewa sun fi sauki a bana.

Raguna sun yi tsada a Kaduna

A Kaduna kuwa, wasu masu sana’r dabbobi shaida wa Aminiya cewa an samu karin farashin dabbobi a bana saboda rufe kan iyakokin kasa da kuma karuwar darajar Dala a kan Sefa.

A cewarsu, yawancin dabbobin ana shigo da su ne daga kasashe makwabta masu amfani da kudin Sefa.

Amma shugaban masu sayar da dabbobi a Kasuwar Zango, Malam Hassan Saleh ya ce a dabbobin ba su yi tsada kamar yadda ake fadi ba, duk kuwa da yanayin da ake ciki.

Wata kasuwar dabbobi a Kaduna

A cewarsa, a kasuwar farashin manyan dabbobi ya fara ne daga N40,000 zuwa 100,000.

“Gaskiya farashin dabbobi ya dan tashi saboda tsadar Dallar Amurka. Domin masu safarar su zuwa cikin kasa sai sun canza kudin zuwa kudin Sefa wanda hakan ke sa farashin tsada.

Aminiya ta fahinci cewa duk da tashin farashin dabbobin akwai kuma yan madaidaita da suka fara daga N18,000 zuwa N35,000.

Malam Muhammadu Siasia ya ce, “Ni na shiga kasuwar ta Zango kuma na samu yan dubu 20,000 masu kyau na saya. Saboda haka karfin aljihun mutum daidai ragon da zai saya”.

‘Masu sayar da raguna na jira a yi albashi’

Manyan dillalan raguna da sauran dabbobi a shahararriyar kasuwar dabbobi ta Kasuwar Shanu a Maiduguri da sauran kananan kasuwanni na kukan rashin masu aikin albashi a kasuwannin.

Modu Kukawa wanda ke sayar da dabbobin a kasuwar wucin-gadi da ke kan Titin Baga ya danganta hakan da rashin biyan albashin ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu.

“Ga raguna nan daban-daban amma babu masu saye. Mutum zai zo kasuwar nan tun ranar Juma’a amma bai wuce ya sayar da raguna uku ko biyar ba a kullum.

“Mun kawo kusan tirela daya ta raguna wannan kasuwar da sauran kasuwanni amma aka shaida mana cewa ba za mu yi ciniki ba saboda gwamnati ba ta yi albashi ba”, inji Modu.

Kudin babban rago a Maiduguri yana kamawa daga N150,000 zuwa N170,000. Matsakaici kuma daga N70000 zuwa N80,000, karami kuma ba ya haura N40,000.

Sai dai Modu ya yi hasashen cewa farashin na iya tashi da zarar aka biya albashi a jihar.

‘Bana dabbobi sun fi tsada a Sokoto

Shugaban kungiyar masu sayar da raguna da awaki na Sokoto Alhaji Isa Bello Unno Sabon Birni ya shaida wa Aminiya cewa bana yanayin kasuwar dabbobi sai godiyar Allah.

“Ba mu fatan farashi ya fi yanda yake a yanzu ba duk da alamu sun nuna babu hakan don an  dauki raguna 1,000 cikin kasuwar nan tamu ta Kara zuwa kasar Nijar

“Kamar yadda muka saba duk sati muna kai musu, dabbobinmu sun fi nasu mai; ga shi kuma kudinsu waton Sefa ta dara farashin Naira.

“A wannan shekarar ma abincin dabbobi ya yi tsada, kan haka farashin dabbobi bai wani haurawa ba, kana iya samun ragon da za ka yi layya da shi a matakin farko N35,000 zuwa N45,000.

“Matsakaici za ka iya samu N60,000 zuwa N100,000, manyan raguna na alfarma kuma N250,000 zuwa N300,000; a haka za ka samu”, a cewarsa.

‘A rangwanta wa masu sayen raguna’

Alhaji Isa ya ce shekara uku da suka gabata kasuwancin ya suya daga yadda a shekarun baya suke fara hada-hadarsu tun sallah saura kwana 30, amma yanzu sati daya ne suke ciniki sosai.

Ya yi kira ga masu sayar da dabbobin a ko ina suke da su sassauta wa masu saye saboda ibada za su yi.

Yusuf Hussain, Jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar masu sayar da shanu ta jihar, ya ce a “wannan shekara an fi sayen Shanun layya fiye da bara.

“Akwai mutum daya da ya zo ya sayi, yan maraka guda 20 a kasuwar nan ta Kara kuma duk layya za a yi da su”, inji shi.

‘’Yan kasuwa sun koka a Legas da Ogun’

Fatake da dilallan dabobbi a jihohin Legas da Ogun na kokawa kan rashin ciniki da suka ce ya addabi kasuwancinsu a bana.

Aminiya ta zanta da ‘yan kasuwa a ziyararta ga kasuwar labar Rago, kasuwar ragunan layya mafi girma a Legas da kuma kasuwar ragunan layya mafi girma a jihar Ogun wato Karar Isheri, kan yadda al’amuran ke tafiya.

Raguna a kauswar Alabar Rago ta Legas

Alhaji Usman Bulama mai sayar da raguna, ya ce sun sayo ragunan da tsada a Arewa sun kawo kasuwannin Legas da Ogun, amma yadda ake tayawa ba ya kaiwa yadda suka sayo dabbobin.

“Mun sayo dabobbin da tsada a Arewa, mun biya kudin mota da tsada mun biya ma’aikata a kan hanya sannan mun zo nan mun iske gari ba kudi”, inji shi.

Ya ce a bara tilas ‘yan kasuwar dabobbi suka karya farashin ragunan layya, kuma hakan na iya faruwa a bana, domin babu masu saya sai daidaiku.

Malam Ibrahim Dumbul mai sayar da ragunan layya a kasuwar karar Isheri da ke mararrabar Legas da Ogun cewa ya yi “masu sauke rago cikin babbar motar tirela 10 a baya, bana da kyar suke iya sauke tirela daya zuwa biyu, saboda tsadar dabbobin a Arewa, “kuma ga shi garin ba kudi, annobar COVID-19 ta lalata komai.

“A baya masana’antu kan zo su sayi ragunan su raba wa ma’aikatansu amma yanzu ba su da halin yin haka.

“Ragon N70,000 a baya yanzu ya zama N150,000 ga shi kuma babu masu saye”, inji shi.

‘Dillalai na iya tafka asara’

Malam Yahaya Garba ya shaida wa Aminiya cewa ya shafe sama da shekara  30 yana sana’ar sayar da raguna amma bai taba ganin dabbobin sun yi tsada kamar bana ba, “ga kuma karancin masu saye, da alamu dillalai za su yi asara ne”.

Malam Yahaya Garba

 “Ragon da muke sayarwa a bara N50,000 a bana N70,000 muka sayo kamarsa tun daga Arewa.

“Ga kudin mota, ko wane rago za ka kashe masa N2,000, banda kudin ma’aikata da muke kashewa a hanya.

“Ga harawa ta yi tsada, don haka nake ganin in ba Allah ne Ya kiyaye ba, za a tafka asara a kasuwar dabobbi a bana”, inji shi.

A zagayen Aminiya a kasuwannin dabobbin Legas da Ogun, kananan raguna na kaiwa N45,000 zuwa N50,000, matsakaita kuma N90,000 zuwa 120, manyan kuma daga N200,000 zuwa sama.

‘Babu turruwar sayen raguna a Kebbi’

Bana ba a samu tururuwar masaya raguna ba a jihar Kebbi, duk da babbar Sallah na kara karatowa.

Aminiya ta zanta da wani dillalin ranguna a kasuwar dabbobi ta Birnin Kebbi, Malam Auwal, wanda ya ce bana farashin raguna ya fara ne daga N35,000 zuwa N150,000.

Wani mai saye da Aminiya ta yi kicibis da shi a karar, Faruk Umar, ya ce duk da ga shi ba masu saye da yawa, amma ragunan sun yi matukar tsada.

Ya kara da cewa, ko wace shekara manyan ragunan layya uku yake saya, amma bana ba zai iya ba saboda sha’anin yau.

Ya ce babu kudi a hanun jama’a don haka zai dai duba dan madaidaici ya saya.

Girki na musamman domin Babbar Sallah

Hadin abinci mai kayatarwa da gamsarwa kuma ya fi wanda aka saba ci da sallah

A duk sadda ake shirye-shiryen Sallah, uwar gida kan so yin girki na musamman da zai kayatar ya kuma gamsar, in da hali ma girkin ya darar abin da ake gani tamkar abincin jiya-i-yau.

Mun yi tanadin yadda za ki yi girkin shinkafa mai kasa da kuma sos din kaza domin kaytar da iyalai da abokan arziki a lokacin bukukuwan Sallah.

Ku ci gaba da bin mu don samun salon girki iri-iri a wannan shafi, amma yanzu ka kwatancen girkinmu na wannan karon:

(1) Shinkafa mai Karas

Kayan hadi:

Shinkafa

Karas

Yankakken attarugu

Albasa

Tafarnuwa

Danyar citta

Kayan kanshi

Farin mai

Sinadarin dandano

Yadda ake yi:

Ki samu shinkafarki ki tafasa ta ki tace da kwando, sai ki ajiye a gefe.

Sai ki yanka karas mai yawa kanana, sannan sai ki tafasa ki tace ki ajiye a gefe.

Ki dauko tukunya ki zuba man girki a ciki sai ki zuba jajjagen citta da tafarnuwa a ciki sai ki soya shi sama-sama.

Sannan ki kawo albasa ki zuba ki, ci gaba da juyawa.

Idan ya soyu sama-sama sai ki dauko shinkafarki wacce ta tsane sai ki zuba a ciki.

Sannan sai ki zuba sinadarin dandano da kayan kanshi a ciki sai ki juya.

Daga nan sai ki dauko tafasasshen karas dinki ki zuba a ciki.

Sai ki dauko attarugu ki zuba a kai domin ya ba shi kanshi na musamman.

(2) Sos din kaza

Kayan hadi:

Kaza

Kayan kanshi

Sinadarin dandano

Attarugu da tumatir

Albasa

Tafarnuwa da danyar citta

Farin mai

Koren tattasai

Yadda ake yi:

Uwargida za ki samu kaza ki yayyanka ta, sai ki tafasa ta da albasa da danyar citta da tafarnuwa da gishiri da sinadarin dandano.

Idan ta dahu sai ki ajiye a gefe. Sannan sai ki yayyanka albasa da attarugu da tumatir da koren tattasai sai ki ajiye su a gefe.

Daga nan sai ki dauko tukunya ki zuba farin mai a ciki ki zuba jajjagaggiyar citta da tafarnuwa a cikin man sai ki dan soya sama-sama.

Sannan sai ki dauko yankakkiyar albasarki ki zuba, sai ki juya.

Daga nan sai ki kawo yankakkun attarugu da tumatir ki zuba a kai.

Sai ki kawo kayan kanshi da sinadarin dandano ki zuba ki jujjuya.

Bayan haka sai ki dauko kazar nan ki zuba a kai, ki jujjuya.

Idan kika gama sai ki dauko yankakken koren tattasanki ki zuba a ciki, sannan ki sa murfin tukunyar ki rufe. Sai ki rage wuta.

Idan kika duba kika ga ya yi shi ke nan sai ki sauke.

Sai a ci wannan sos din kazar da shinkafa mai karas.