✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ayade ya kori kwamishinoni saboda kin komawa APC

Gwamnan ya sallami kwamishinonin da hadimansa saboda kin sauya sheka tare da shi.

Gwamnan Jihar Kuros Roba, Ben Ayade, ya sallami kwamishinoni hudu da masu ba shi shawara ta musamman biyar, saboda sun ki sauya sheka zuwa sabuwar jam’iyyarsa ta APC.

Sanarwar sallamar da Sakataren Yada Labaran Ayade, ya fitar a safiyar Litinin, ta umrace su da su dawo ga gwamnatin jihar duk kayayyakin ta da ke hannunsu da suka hada da motoci, gidaje da sauransu.

Kwamishinonin da gwamnan ya sallama sun har da Rita Anyim wadda take da kusancin da tsohon gwamnan jihar, Liyel Imoke da wasu ’yan jam’iyyar PDP.

Hadiman gwamnan da ya sallama kuma sun hadar da Leo Iyambe, Orok Otu Duke, Victor Okon (Alausa), John Etim Bassey da Agbiji Mbeh Agbiji.

Kwamishinonin sun bayyana rashin jin dadinsu game da hukuncin da Gwamna Ayade ya yanke na barin jam’iyyar PDP zuwa APC.

Alamu na nuna cewa da yawa daga cikin kwamishinoni da hadimai wanda sauya shekar bai musu dadi ba, za su iya barin gwamnatin tasa.

Gwamnan ya gana da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a ranar Asabar kan yadda za a ba da mukamai ga ’ya’yan jam’iyyar a gwamnatin tasa.