✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ayu bai isa ya musanta karbar cin hancin N1bn ba —Wike

Wike yi yi tir da ikirarin cewa dan takarar Shugaban Kasa na PDP, Atiku Abubakar, cewa dan takarar ya gina gadoji a sassan Najeriya.

Gwamnan Jihar Ribas, Nyensom Wike ya ce, musanta zarginsa da Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Dokta Iyorchia Ayu, ya yi, abu ne mara tushe balle makama.

Wike ya kuma yi Allah wadai da ikirarin da ake dangantawa da dan takarar Shugaban Kasa na PDP, Atiku Abubakar, cewa dan takarar ya gina gadoji a sassan Najeriya.

Wike ya yi wadannan bayanan ne jim kadan da dawowarsa Najeriya bayan tafiyan kwana uku da ya yi zuwa kasar Spaniya.

Kwannan nan ne aka ji Wike ya yi zargin Shugaban PDP na Kasa, Dokta Ayu, ya karbi cin hanci na Naira biliyan daya daga hannun wani dan takarar da ba a bayyana ko wane ne ba.

Ayu ya ce kudin da Wike ke zargin, kudi ne da aka so ciyo bashi daga banki domin gudanar da harkokin jam’iyya wanda daga bisani aka janye kudurin karbo bashin.

Dangane da batun Atiku ya gina gadoji kuwa, Wike ya bukaci PDP ta fito ta bai wa ‘yan Najeriya hakuri saboda a cewarsa, babu wani aiki da Atikun ya yi makamancin haka a kasa.

Wike ya tafi taro a Spaniya ne tare wasu takwarorinsa da suka hada da Gwamna Okezie Ikpeazu na Jihar Abia da Samuel Ortom na Jigar Binuwai da kuma Senyi Makinde na Jihar Oyo.